SHAFIN FARKO ...I.... GAME DA MU.....I....SHARHIN FIM.....I.....ADABI.....I.... WASIKU.....I... TUNTUBE MU

TABA KA LASHE
DAGA ZUCIYA
RAYUWAR IYALI
KWALLIYA DA GYARAN JIKI
GAJEREN KIRKIRARREN LABARI
 
A MUJALLAR & FIM TA WATAN GOBE
Me ya sa su MUTUWA DOLE suka kafa Kungiyar AHFIP?
'Karambanin' Farfesa Abdalla a Industiri! Ku biyo mu!>>

 
A FILM BY ABDALLA UBA ADAMU
DIRECTED BY
Bala Anas Babinlata
Visually Ethnographic Productions, 2009
Kano,
Northern Nigeria


YADDA AKA SO BUDE WA ’YAN FIM WUTA A JOS
AN ce tsautsayi in ya wuni ba ya kwana.
A ranar Asabar, 26 ga Yuni 2010, wasu ’yan fim su ka tsallake rijiya da baya a Jos, Jihar Filato.
Matsa nan don ci gaba.


RASHEEDA TA DEBO DA ZAFI A KATSINA
* An hana furodusoshi yin fim da ita, sannan darakta zai maka ta a kotu.
Matsa nan don ci gaba.

DAGA ZUCIYA Tare da NABEELA IBRAHEEM KHALEEL

Kayan da’a (2)


Haramtattun Kayan Da’a

WADANNAN sun kasu gida biyu: akwai wadanda ba su da inganci saboda haramun ne a yiamfani da su a Musulunci; akwai kuma wadanda ba su da inganci saboda su na zama cutarwa ga ma’aurata. Don haka ’yan’uwa na mata a kula da kyau, duk kayan da’ar da zan jero a kasa, a yi kokari a kiyaye amfani da su saboda cutarwar da za su haifar ya ninka amfanin da su ka iya yi ninkin-ba-ninki.

*Duk kayan da’ar da za a hada wa mace don ta mallake mijin ta ya zamana ba ya jin dadin saduwa da kowa sai ita to haramun ne, domin dole sai da sihiri ne za a iya hada shi, kuma sihiri harumun ne, sannan shirka ce babba, ba ta hanyar da Musulmi ya halatta ya yi amfani da shi kuma duk wanda ya mutu ya na mai aikata shi, to rahamar Allah ta haramta a gare shi. Allah SWT Ya fada a Aya ta 69 cikin Suratul D.H: “Kuma masihirci ba ya cin nasara a duk inda ya je”.

Don haka kada uwargida ta dauka mallake maigida da tsibbu a matsayin cin nasara. Wallahi asara ce babba inda dai ki na sani domin ga shi da kin karanta kuru-kuru Allah SWT Ya fadi sakamakon masihirta. Sannan wannan ya zama cutarwa ga maigida domin tauye masa hakkin sa da damar da Allah Ya ba shi na nuna so da sha’awa ga mata har hudu ba daya kawai ba. Haka kuma cutarwa ga abokiyar zama na danne mata hakkin ta na samun soyayya da nuna sha’awa daga mijin auren ta.

*Duk wani kayan da’ar da aka sa wasu sharudda ga kayan hada shi ko ga yadda za a hada shi ko kuma ga yadda za a yi amfani da shi. Misali, wanda za a ce a nemi itace mai saiwa waje, itacen kan itace, tsiron da ya fito cikin kahon sa, ko a ce a dafa tsoka 99 kuma a tanadi allura 99 kowace tsoka daya a ci ta da allura daban, ko gumba dunkule uku a dama da nono farar saniya kuma in an sha ba a magana. Ko a kunshe gero cikin baki a kwana da shi, sai da safe a dake garin sa a rinka barbada wa miji cikin abinci, ko a ce in miji fari ne a dafa farar kaza a ci, in kuma baki ne a dafa bakar kaza. Ko kazar da za ce ba a tauna kashin ta sai dai a yi rami a rufe. Ko wanda za a ce in an sha ba a kwana da miji sai bayan wasu kididdigaggun kwanaki, ko wanda za a ce a sami mahaifar jaki, madaciyar kaza, al’aurar saniyar da ba ta taba haihuwa ba, dai ire-iren wadannan. Duk wannan sharudda ne da shaidanun aljannu ne ke gindaya su in an yi masu sai su biya wa mutum bukatar sa. Uwargida ta sani, in ta yi haka ta janyo shaidanu ne su rinka tarayya da ita lokacin da ta ke saduwa da mijin ta; to yaushe ta ke fatar samun natsatstsen yaro da saduwa irin wannan?

*Duk wani kayan da’ar da za a hada shi tare da wasu ayoyi na Alkur’ani Mai Girma shi ma tsibbu ne. Misali, wanda za a ce a rubuta wani hatimi da sunan miji da mata a ciki, a wanke a ba kaza ta shanye ruwan, sannan a yanke kazar, a dafe ta da wani ruwan rubutun hade da wasu magunguna. ko a wanke wata aya ta musamman daga cikin ayoyin Kur’ani masu tsarki, a hada ruwan rubutun a yi dan matsi da shi mace ta sa a cikin farjin ta. Da wasu makamantan irin wadannan.

*Akwai wanda mace za ta yi tsarki, ta tare ruwan tsarkin nan, ta yi miya da shi ta ba mijin ta ya sha don ta mallake shi. Shi ya sa dai ba a arzikin da ya kai samun mata tagari ga da namiji domin kariya ce gare shi daga duk irin wadannan abubuwan kazanta da najasa da kafirci.

*Akwai turaren da ake hada mace, kuma don mijin ta kawai ake hada shi, kuma ba a son kowa ya yi amfani da shi sai ita kadai, kuma ba a son kowa ya ji kamshin sai mijin kadai.

*Akwai sa-kishiya-kuka, wanda in mace ta yi amfani da shi, in miji ya sadu da mace, washegari zai saki kishiyar ta. Wannan haramun ne kuma babban hadari ne kwarai da gaske domin Annabin Rahma SAW ya fada cewa: “Duk wanda ya aikata wani abu wanda ya yi sanadiyyar rabuwar miji da mata, tsinuwar Allah sun tabbata a kan shi daga duniya har lahira kuma Allah SWT Ya haramta mashi kallo zuwa ga Fuskar Sa Mai Girma ranar gobe kiyama.”

*Akwai wani kwallin kayan da’a wanda in mace ta shafa shi su kai ido hudu da mijin, to ta mallake soyayyar shi da sha’awar sa kenan. Wani akan hada shi da dabino, kukunniya da majinar bango, wani kuma sai a ce mace ta bayar da gashin kan ta na hammata da na al’aurar ta a hada mata wannan kwalli da shi. In aka lura, duk ire-iren sharuddan da shaidanu kan gindaya ga malaman tsibbun da su ke yi wa hidima ne.

*Akwai wanda in mace ta yi amfani da shi ya na haukatar da mijin ta lokacin gudanarwar ibadar auren su har ya yi maganganu da surutan da bai ma san ya yi ba. Irin wannan akwai tukunyar karatun mata, wanda a ke tsima wasu itacen da aka gindaya wa sharudda a cikin tukunya kuma da murfin tasa ne kadai za a iya rufe tukunyar, mace da wannan ruwan kadai za ta rinka tsarki kuma duk lokacin da ta bude tukunyar to za ta yi jifa ne da murfin, to wai kamar wannan kara haka mijin zai haukace lokacin ibadar aure. Haka nan akwai cije kunne, wanda tsanani zautuwa zai sa miji ya cije kunnen matar sa. Akwai kuma karamar kyauta: gida, ko mota ko kujerar Makka, shi kuma wannan duk abin da mace ta tambayi miji zai yi alkawarin ba ta ko da bai da abin nan. Da dama ya jefa maza da yawa ga yin kyautar dole ya kuma raba aure in aka yi rashin sa’a maigida ya ki cika alkawarin da ya yi cikin fitar hankalin sa.






Shafin Farko


An fara buga mujallar Fim (ISSN 1595-7780) a cikin Maris 1999. Ta na fitowa a kowane wata daga kamfanin INFORMART PUBLISHERS LTD., No. AK 6, Yoruba Road, Kaduna, Nijeriya. Ofishin mu a Kano: Ofishin mujallar Concern, 2nd Floor, Hadiza House, daura da Masallacin Umar Ibn Khattab, Zaria Road, Kano.
A aiko da dukkan wasiku ta adireshin mu na I-mel: mujallarfim@yahoo.com