SHAFIN FARKO ...I.... GAME DA MU.....I....SHARHIN FIM.....I.....ADABI.....I.... WASIKU.....I... TUNTUBE MU

TABA KA LASHE
DAGA ZUCIYA
RAYUWAR IYALI
KWALLIYA DA GYARAN JIKI
GAJEREN KIRKIRARREN LABARI
 
A MUJALLAR & FIM TA WATAN GOBE
Me ya sa su MUTUWA DOLE suka kafa Kungiyar AHFIP?
'Karambanin' Farfesa Abdalla a Industiri! Ku biyo mu!>>

 
A FILM BY ABDALLA UBA ADAMU
DIRECTED BY
Bala Anas Babinlata
Visually Ethnographic Productions, 2009
Kano,
Northern Nigeria


YADDA AKA SO BUDE WA ’YAN FIM WUTA A JOS
AN ce tsautsayi in ya wuni ba ya kwana.
A ranar Asabar, 26 ga Yuni 2010, wasu ’yan fim su ka tsallake rijiya da baya a Jos, Jihar Filato.
Matsa nan don ci gaba.


RASHEEDA TA DEBO DA ZAFI A KATSINA
* An hana furodusoshi yin fim da ita, sannan darakta zai maka ta a kotu.
Matsa nan don ci gaba.



SAKON TA’AZIYYA
Daga Hajiya Hassana,
Kaduna. 08033581119
INA so ku isar da sakon ta’aziyya ta ga ’yan’uwa da abokan sana’ar marigayiya Safiya Ahmed. Allah Ya gafarta mata. Ya sa Aljanna Firdausi ce makomar ta. Mu kuma da mu ka rage, Allah Ya kyautata karshen mu. Rukayya Dawayya da Rasheeda Adam Allah Ya saka maku da alheri. Maryam Hiyana ki na cikin addu’a ta ko da yaushe, kuma har abada. Da fatan ki na nan ki na yi wa mijin ki ladabi da biyayya kamar yadda mu ma mu ke yi wa mazajen mu. Allah Ya kara maku so, kauna da yarda da juna. Jinjina gare ka jarumi na, Ibrahim Maishunku. Allah Ya kara maka basira.

A GAIDA GWANAYE NA
Daga Bashir Ahmad,
Bodinga, Jihar Sokoto. 08032878618
INA son edita ya isar min da gaisuwa ta ga Maryam Booth, Sakna Gadaz da kuma Fati Washa. Allah Ya kara masu daukaka. Ya kuma ba su mazaje nagari.

ALLAH YA BADA ZAMAN LAFIYA
Daga Muhammad G. Tafeeda Tangaza
eazytangaza@yahoo.ca
08035916476

EDITA, ina kara godiya kan irin damar da ka ke ba mu a wannan mujalla mai matukar farin jini ina kara godiya kan wannan kokarin, Allah Ya karo ci-gaba mai amfani.
Wannan karon na rubuto ne domin in taya babban jarumi Abba El-Mustapha da amaryar sa murnar auren su ina masu fatar Allah Ya ba da zaman lafiya, zuri’a dayyaba da sauran alhairan da ke kunshe cikin raya Sunnar Ma’aiki. Su kuma wadanda har yanzu ba su cimma lokaci ba sai in ce Allah Ya hada kowa da rabon sa mai amfani. Na gode.

A GAIDA JALINGO DA BOOTH
Daga Maryam Attahiru (Ummi),
’Yankuzo, Jihar Zamfara.
08055604222
INA jinjina ga Musa Jalingo da Maryam Booth saboda fadakar da ’yan’uwan mu mata a kan biyayyar aure a cikin fim din ‘’Yar Aljanna’. Allah Ya saka masu da alheri. Gaisuwa ga Khadijatul Iman Sani Danja.

INA NEMAN SANI
Daga Armaya’u Aminu,
Kaita, Jihar Katsina.
07031131693
EDITA da ’yan’uwa na masu karatu ina fatan kowa ya na lafiya. Na ga hira da aka yi da Fati Yola. Sai na ji ta ambaci marigayi Aminu Bala. Shi ne na ke tunanin ko dai Ali Bala ta ke nufi? Ko shi ma Aminu Balan ya rasu ne? Edita ina son a fahimtar da ni.
Ba shakka Ali Bala ta ke nufi. Aminu Bala na nan da ran sa. Mun gode.

GYARA A RANTSUWA
Daga Fati Adam,
Bauchi. 08020740495
GAISUWA ga mujallar Fim. Don Allah gyara ne na ke so in yi wa ’yan’uwa Musulmi, musamman ’yan fim. Yawanci a cikin finafinai su kan yi irin rantsuwar nan su ce don Allah don Annabi. Kuskure ne babba hada Allah da Manzon Sa, bayan ba a hada Allah da wanin Sa. In mu ka ce don Allah kadai ya wadatar. Da fatan za mu gyara.

KUN YI RAWAR GANI
Daga Yahaya Easy,
Bakin Kura, Jihar Bauchi.
08020965923
JINJINA da fatan alheri ga wannan mujalla ta Fim da kuma jinjina ga daukacin ’yan fim da su ka yi hobbasa wajen ganin sun kwaci ’yancin su daga wajen mayaudari mai ci da addini. In da a ce su na tabuka makamancin haka, da ba su kai ga halin da su ke ciki a yanzu ba. Ina nufin yunkurin da su ka yi a Kaduna. Gaisuwa ga Aliyu Gora II da Sani Musa Danja.

LERE KA SHIRYA WANI
Daga Yahaya M. Nahuche,
Jihar Zamfara. 08133239850
DA fatan dukkan ma’aikatan mujallar Fim su na lafiya. Ina son in yi kira ga gwani na, wato babban furodusa Yakubu Lere. Fim din ‘Wasila’ fim ne da ya shahara, wanda ba ma masu tasowa ba, ko wanda ba a haifa ba zai zo ya same shi. Maimakon sake shirya shi, a nawa ganin, gara tunanin yin wani labarin daban. Ina mika godiya ta ga Aliyu Gora II da Fati Slow.

SAKON TAYA MURNA
Daga Fatin Marwana,
Gusau, Jihar Zamfara. 08027996315
INA taya Ali Nuhu murnar samun nasarar cin gasar ‘SIM Awards 2010’ a matsayin ‘Best Hero’. Allah Ya kara daukaka. Gaisuwa ga gwanaye na irin su Zainab Indomi, Jamila Nagudu, Fati KK, Rahama Abuja, da sauran su.

KU DAUKI MATAKI
Daga Ramatu S. Bala,
F.C.E. Kontagora, Jihar Neja.
08054020566
SHIN iyayen Zainab Indomi su na sane da halin da ta ke ciki kuwa? In ko su na sane, ya kamata su gaggauta daukar mataki a kan ta. Ma’ana su zaunar da ita su yi mata nasiha. Domin wani lokaci za ka ga mutum ya san gaskiya amma sai ya take, ya yi ta yin abin da ran sa ke so. Gaisuwa ga jarumi na Ali Nuhu, angon Maimuna. Allah Ya raya su a kan tafarkin Manzon Allah (S.A.W.).

MU NA FA KUSKURE
Daga Abdullahi Babawuro,
08135622908
INA fatan edita zai ba ni dama a cikin wannan mujalla mai farin jini da tarin albarka, don in yi kira ga ’yan’uwa na masu karatu maza da mata da su daina kiran lambobin mutane da su ka gani a mujalla. Domin ni na ga matar auren da ta rika kiran aboki na har zancen so ya shiga tsanin su, amma shi bai san matar aure ba ce sai daga baya. To kun ga wannan abu da me ya yi kama? Kuma abin ya fi faruwa ga mata. Don mu maza da mun ga lambar mace sai mu dauka mu kira ko mu tura sako mu na son su. Don Allah mu gyara.

SAKON GAISUWA
Daga Fatima Ahmad,
Jihar Jigawa. 08030836786
INA mika gaisuwa da fatan alheri ga mujallar Fim. Gaisuwar ban girma ga Zainab Indomi. Ina kuma son edita ya ba ni lambar ta in da hali.

’YAN FIM KU GYARA
Daga Jamila Bello,
Gusau, Jihar Zamfara. 08085328786
GAISUWA da jinjinar ban-girma ga edita da ma’aikatan mujallar Fim. Wannan karon zan yi kira ne ga ’yan fim baki daya da su yi wa Allah su dinga kwaikwayon halayen kwarai, musamman mata. Kada su dauka daga duniya sai Kaduna; a’a, akwai lahira gidan hisabi. In ka yi mai kyau, ka ga da kyau. In ka yi maras kyau, ka ga maras kyau. Allah Ya sa mu dace, Ya kuma ba mu ikon gyarawa baki daya.

KU BA NI LAMBAR SU
Daga Shafa (Mrs),
Jihar Zamfara. 08065868774
ALLAH Ya kara maku daukaka mujallar Fim. Allah kuma Ya biya ku, Ya kuma kara basira da hazaka. Don Allah edita ina son ka taimaka min da lambar wayar Fati KK da Jamila Nagudu. Ni matar aure ce, amma su na burge ni.

’YAN FIM GA NASIHA
Daga Ibrahim Shika,
Magajin Gari, Jihar Kaduna.
08024146739
INA kira ga dukkan wanda ya ke sana’ar fim da cewa gaskiya ya kamata ku rika rufa wa kan ku asiri. Ku daina tona wa junan ku asiri, domin tona wa junan ku asiri ba zai haifar maku da da mai ido ba. A karshe, ina mika jinjina ta ga madugu uban tafiya, wato Ibrahim Sheme, da kuma Aliyu A. Gora II, Abba Muhammad da sauran su.

KU SA NI A HANYA
Daga Abubakar Abdullahi.
Jihar Kaduna. 08037328294
GAISUWA tare da fatan ku na lafiya. Edita, wai me ke hana Ali Nuhu halartar bukukuwan abokan harkar sa? Domin na sha sa ido ko zan gan shi a wurare da yawa da ya kamata ya halarci wurin, amma sai ya kasance bai je ba. Gaisuwa ga ma’aikatan mujallar Fim.

GARA HIYANA DA ZEE-ZEE
Daga A’isha Little Eesha,
08061391560
ALLAH sarki Maryam Hiyana! Sai yanzu aka san gara abin da ya faru da Hiyana a kan rayuwar Ummi Zee-Zee? A yanzu mu dai fatan mu Allah Ya kara mata zaman lafiya da mijin ta. Allah kuma Ya kara dankon soyayya a tsakanin su, Ya kuma raya maku dan ku. Ita kuma Ummi Zee-Zee, Allah Ya shirye ta. Gaisuwar ban-girma ga umma ta Hajiya Hassana da kanwa ta Rukayya. Jinjina ga Ali Nuhu, Mahmud Nagudu, Ali Jita, Jamila Nagudu, Zainab Indomi, da Maryam Jibril. Gaisuwa ta musamman gare ka masoyi na mai kwantar da zuciya ta a kowane lokaci.

A RIKA SARA...
Daga Mrs Kinafa,
07035871677
DA fatan ma’aikatan mujallar Fim ku na lafiya? Ina so don Allah ku ba ni dama in mika jinjina ga kamfanin FKD kan fim din ‘Ahali’ da ‘Sai Wata Rana’. Gaskiya ku na kokari, Allah Ya kara fasaha. Bayan haka, na kalli wani fim na Turanci mai suna ‘Spirit of a Dancer’, wanda Ali ya yi. Gaskiya a rika sara ana duban bakin gatari. Daga karshe, ina gaida Jamila Nagudu, Maryam Booth, da Zainab Indomi; sai kuma kanwa ta Maman Nabil da Muhseen.

KU SADA NI DA BOOTH
Daga Basheer,
Jihar Sokoto. 07031947494
DON Allah edita ina son ku sada ni da gwana ta, wadda ba na sha’awar duk wani fim da ba ta ciki, wato Maryam Booth. Don Allah edita ka mika min sako na gare ta. Ke kuma don Allah Maryam ki yi min ko da filashin ne da wannan lambar. Mujallar Fim na yi maku alkawarin rokon Allah Ya daukaka ku na tsawon wata daya. Jinjina ga Zainab Indomi da Nafisa ‘Sai Wata Rana’.

LERE KA SAKE TUNANI
Daga Bilkisu Tahir,
Gusau, Jihar Zamfara. 08069561848

WASU Allah Ya yi masu gajeren tunani. Lere, meye ba ka samu ba a fim din ‘Wasila’ da ka ke kokarin sake shirya shi? Kai, ba ma Hausawa ba, hatta sauran yaren Nijeriya da ba sa jin Hausa ka yi masu na Turanci kuma sun kalla. To meye ka ke so ka nuna mana kuma? Ka sake tunani Yakubu Lere.

KU DAINA SUKAR JUNA
Daga Rabi’u Agege,
Agege, Jihar Legas. 08029443333
NA ji an yi hira da wasu ’yan wasa a mujalla sun nuna sukar Awards da wasu su ka samu. Ina ba ku shawara, duk lokacin da wani a cikin ku ya samu ci-gaba ku dauka kamar dukkan ku ne ku ka samu. Saboda son juna da hadin kai. Domin ku sani, ko rabon kudi ake yi wani ba ya samu. Kuma ku duba ko yatsun ku ba daya ba ne. Don Allah ku gyara.

A GAIDA MUJALLAR FIM
Daga Farida Bello,
Dogondaji, Jihar Sokoto. 08027483300
INA son in yi amfani da wannan dama in mika jinjina ta ga mujallar Fim, musamman kan yadda ta ke tsara abubuwan ta bisa tsari da kuma fede gaskiya komai dacin ta. Kin yi taki kin yi ta raggo, kin yi ta mai dan karfi! Gaisuwa ga Aliyu A. Gora II da sauran ma’aikatan mujallar Fim.

ALLAH GAFARTA MATA
Daga Fatima Yarima,
Damaturu, Jihar Yobe. 08067545687
INA so a mika min sakon ta’aziyyar rasuwar jaruma Safiya Ahmed ga iyaye, ’yan’uwa da abokan arziki. Allah Ya jikan ta, Ya ba dangin ta hakurin jure wannan babban rashi da su ka yi. Gaisuwa ga jaruma ta, Fauziyya Mai Kyau.

KU BA MU LABARIN KUBRA
Daga Hadiza M.,
Old Airport Road, Minna, Jihar Neja.
07081424067
INA taya mujallar Fim murnar cika shekaru 11. Sannan ina son ku ba mu tarihin Hajiya Kubra, wadda ta yi wakar ‘Sarkin Fulanin Gombe’. Wasu sun ce sarkin ya aure ta. Don Allah ku samo mana labarin. Allah Ya taimake ku.

A GAIDA ’YAN KADUNA
Daga Murtala Salihu,
Gada, Jihar Sokoto. 08037350483
TARE da fatan edita zai ba ni dama a cikin wannan mujalla mai farin jini domin in yi jinjina ga ’yan fim din Kaduna a kan barazanar da su ka yi wa Rabo dangane da hirar da ya yi a gidan talabijin na DITV. Kuma ina mai ba da shawara ga ’yan fim masu goyon bayan Rabo da su yi hankali, domin bai dace a ce ku na son cin mutuncin ’yan’uwan ku wadanda ba su yi mubayi’a da gwamnati ba, kamar yadda Ahlan ya yi wa Afakallahu, amma daga karshe bai sha da kyau ba.

NA SAMU MASOYIYA
Daga Aliyu M. Al-Ameen,
07081621522
A RAYUWA ta duniya ba ka san inda za ka hadu da masoyin ka ba. Dalilin wani abu sai ka ga Allah Ya hada ka da irin wanda ka ke so. Ni dai yanzu dalilin mujallar Fim na hadu da wadda na ke so, ita ma ta ke so na. Ina alfahari da ita. Ina son ’yan’uwa su taya mu da addu’a. Ina kuma rokon Allah Ya kara daukaka mujallar Fim. Gaisuwa ga jarumin jarumai, Sarki Ali Nuhu, da Adam A. Zango, Sadiya Gyale, Jamila Nagudu, Adamu Nagudu, da sauran su.

JAMILA NAGUDU FA?
Daga Sameera Bello,
08029002377
GAISUWA da fatan alheri ga ma’aikatan mujallar Fim. In dai har za a iya ba Ibrahim Maishunku kyautar jarumin jarumai da fim din ‘Jamila Da Jamilu’, to ban ga dalilin da zai hana a ba Jamila Nagudu jarumar jarumai mata ba saboda ta ma fi shi wasa a fim din, don ita ce jigon fim din. Ta cancanci ko da ba a ba ta jarumar jarumai ba, ai za a iya ba ta matallafiyar jaruma. Fim din ya karbu wajen jama’a. Kafin na 3 ya fito har wadanda ba su damu da fim din Hausa ba za ku ji su na tambaya yaushe na 3 zai fito? Amma ban ce bai kamata a ba Maishunku ba. Amma ita Jamila ta fi shi shan wahala. Ita ta isar da sakon da fim din ke dauke da shi.

KU DAINA KIRAN SU
Daga Fatima Larai,
Yelwa, Jihar Kebbi.
INA kira ga wasu maza da ke kiran lambar mata wai don sun ga lambar su a mujalla sai su kama kira ko ba su san mai shi ba. Kuma ba su sani ko matar aure ce ko a’a ba. Don Allah su bari, don in aka yi wa matan su haka ba za su ji dadi ba. Ina kira a gare su da don Allah su bari.

A DAINA TUNA BAYA
Daga Murja Isiyaku,
Army Barracks, Sokoto. 08036099510
YA na da kyau duk bil’adama ya yarda da kaddara a kan abu mai kyau ko maras kyau. Dangane da abin da ya faru ga Hiyana, bai kamata ana tuna baya ba. Amma da zarar industiri ta samu matsala, maimakon su yi kokari su gyara sai ka ji an ce tun lokacin hayaniyar Hiyana. Don Allah jama’a mu daina tuna baya. Kuma a daina ambatar sunan Hiyana. Domin gara ita bisa ga wasu.

AKWAI FA MUTUWA
Daga PC Ibrahim,
Unique Studio, W/Dada,
Jihar Bauchi. 08086684525
INA son in yi amfani da wannan dama in ja hakalin ’yan matan industiri. Saboda irin munanan dabi’un da su ke yi na sa kananan kaya da kuma kona gashi. Wanda lokacin da su ka zo ba haka su ke ba. To kar su manta da cewa akwai mutuwa.

A GAIDA MA’AIKATAN FIM
Daga Zee M. Tahir,
Kaduna. 08024158209
GAISUWA da fatan alheri ga dukkan ma’aikatan wannan mujalla mai farin jini. Ina jinjina ga Ummancy Umar da Zuwairiyya Girei dangane da ilimin da su ke kara wa jama’a a cikin wannan mujalla mai tarin albarka. A karshe ina mika gaisuwa ga Jamila Nagudu da Dr. Musty Usama Kebbi.

LAIFIN MANYA NE
Daga Alkamis Sulaiman,
Gidan Takai, Jihar Taraba.
08069703315
EDITA, ina so ka ba ni dama don in tofa albarkacin baki na kan matsalolin da ake samu tsakanin ’yan fim da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano. Ni a gani na, wannan ya faru ne saboda janyewa ko rikon sakainar kashin da wasu jigajigan kamfanoni su ka yi. Ka ga kamar Mandawari Enterprises, Sarauniya Films, Iyan-Tama Multimedia, Lerawa Films, da Gidan Dabino International. Lokacin da wadannan kamfanonin ke tashe, su na rubuta labarai masu ma’ana da nuna al’adar Hausa da addinin Musulunci.

KADAN KI KA GANI
Daga Aminu Alhassan Koki,
Jihar Kano. 08098683848
Fati Shuwa na ji kin ce Misbahu ya yaudare ki. Tsakanin ki da Allah kafin Misbahu ya fara soyayya da ke, maza nawa ki ka yaudara? Ina ce kafin ki shigo harkar fim mijin auren ki ki ka tunkude ki ka shiga harkar fim? Fati, kadan ki ka gani. Darajar ’ya mace dakin mijin ta. In kuma an ki sharar masallaci, a yi ta kasuwa.

BA KI KYAUTA BA
Daga Ibrahim Isah,
Zariya, Jihar Kaduna, 08037664445
ZAINAB Indomi ki ji tsoron Allah, domin akwai mutuwa. Irin yadda hoton ki ya bazu a duniya da rigar nono, kuma an rubuta Me Sexy ba daidai ba ne ga ’yar Musulmi. Ki sani, ba yanzu ake ji maki ba, gaba ake ji maki.

HUKUNCIN YA YI
Daga Alhaji Ghali Muktar
DON Allah Edita ka ba ni dama a cikin wannan mujalla mai farin jini domin in bayyana goyon baya na dangane da hukuncin da hukumar Rabo ta dauka a kan Maryam Booth cewa an yi daidai. Domin wallahi yanzu ne lokacin da ya kamata ta yi aure don ta ji dadin kuruciyar ta a matsayin ta na matar aure. Kuma ina daga cikin masoyan ta na tsakani da Allah. Ina rokon Allah Ya ba ta miji nagari.

KUSKURE A FIM TA MAYU
Daga Yusuf Ubale,
UBD Road, Kano. 08037054040
GAISUWA ga dukkan ma’aikatan mujallar Fim mai fari jini da kokarin fayyace halin da ’yan fim ke ciki. Jinjina ga makaranta wannan mujalla da kuma ’yan fim baki daya. Ina sanar da mawallafa wannan mujalla cewar injin bugawa ya tsallake shafi na 6 da 51 a Fim ta Mayu 2010, wanda dukkan su su na da muhimmanci. Da fatan za a dauki matakin da ya dace.

Malam Yusuf, ba laifin injin ba ne kamar yadda ka ce. Hakan na faruwa ne a lokacin da ake harhada shafukan bayan an gama bugawa. - Edita

NA YABA DA FILAYEN
Daga Mallam M. Surajo,
Layin Mudi, Oniwaya, Agege, Lagos. 07065022222
NA rubuto wannan wasika ne domin in jinjina maku game da kokarin da ku ke yi na wayar wa al’umma kai game da lamarin rayuwar su da addinin su. Ina matukar jin dadin bayanan ku da ku ke aiko mana, musamman filin Nabeela Ibraheem Khaleel da Ummancy Umar. Ina fatan za ku karo mana wasu masu hazaka irin su.

KU DAINA YAUDARA
Daga Kurama Abubakar,
Abuja. 08055940482
A GASKIYA ’yan fim ku daina yaudara a maganar aure. In har ba za ku iya auren junan ku ba, ku daina yin soyayyar da har jama’ar gari za su sani. Ku yi koyi da Shu’aibu Kumurci da marigayiya Balaraba Mohammed, marigayi Ahmed S. Nuhu da Hafsat Shehu, Hassan Giggs da Muhibbat Abdussalam. Soyayyar su babu yaudara da cin amana. Amma ku dubi soyayyar Misbahu da Rukayya Dawayya, Sani Danja da Maryam Jankunne, Lawan Ahmad da Fati Mohammed, Adam A. Zango da Maryam Booth, Aminu Ala da Maryam Baba, da kuma Abbas Sadiq da Zainab Idris. Idan kun duba, abin kunya ne a gare ku.

ZAN AURI KAWU KAMFA
Daga Fa’iza,
Kaduna. 08132510288
ALLAH Ya kara maku daraja, Ya kuma kare ku daga makiyan ku! Na ji labarin Kawu Kamfa an raba shi da masoyiyar sa. Ina son ku sanar shi cewa zan maye mashi gurbin ta a zuciyar sa. Saboda ni ma na rasa nawa masoyin, amma shi ya riga mu gidan gaskiya ne. Allah Ya jikan shi da rahama. Wannan lambar ita ce lamba ta, ku ba shi.

A GAIDA GWANAYE NA
Daga A’isha M. Korafi,
Kwaru, Badarawa, Kaduna. 07034992416
INA son Editan wannan mujalla mai farin jini da albarka ya ba ni dama in mika gaisuwa ta ga jarumai na irin su Zainab Indomi, Jamila Nagudu, Ali Nuhu, da Mahmud Nagudu.






Shafin Farko


An fara buga mujallar Fim (ISSN 1595-7780) a cikin Maris 1999. Ta na fitowa a kowane wata daga kamfanin INFORMART PUBLISHERS LTD., No. AK 6, Yoruba Road, Kaduna, Nijeriya. Ofishin mu a Kano: Ofishin mujallar Concern, 2nd Floor, Hadiza House, daura da Masallacin Umar Ibn Khattab, Zaria Road, Kano.
A aiko da dukkan wasiku ta adireshin mu na I-mel: mujallarfim@yahoo.com