Ko Giggs Zai Kara Fadawa Ragar Kauna?
< 
AN ce so hana ganin laifi. Kowa ya san a baya an sharbi soyayya tsakanin darakta Hassan Giggs da jaruma Zainab Raga. Ana kuma sane da yadda su ka rabu dutse a hannun riga, har aka yi masu tsakani a wani barikin sojoji da Zainab din ta kai karar sa wajen wani saurayin ta. Kun san an ce in da ran ka, ka sha kallo.
Kwanan nan wakilin mu ya ci karo da masoyan biyu a Katsina wajen daukar wani fim na Abdu Boda, wanda kuma shi Giggs din ne darakta. Amma wakilin namu ya samu labari, da farko ba Zainab ce jarumar shirin ba. Sai ga shi ta zama wuka da nama a daukar fim din. Tambayar da ta yawaita a wurin ita ce: yaushe aka shirya tsakanin Raga da Giggs? Sai dai wakilin mu ya samu amsar a sama, lokacin da ya ziyarci shagon furodusa Baba Karami a Kano.
Su na zaune hirar Raga da Giggs ta taso. Sai shi Baba Karami ya dubi Giggs ya ce, “Wai ko dai ungulu za ta koma gidan ta na tsamiya ne?”Sai shi kuma daraktan ya amsa da cewa, “Gaskiya idan ita Zainab ta na kan bakan ta na soyayya, to ni yanzu na manyanta, tunda na fara aje iyali.”
Shi dai Giggs, bayan rabuwar sa da Raga, jaruma Muhibbat Abdussalam ya aura, kuma sun haifi kyakkyawar ’yar su wadda su ke ji da ita kamar me.
Bayan an bushe da dariya a shagon Baba Karami, sai wani Alhaji da ke wurin ya tofa albarkacin bakin sa da cewa, “Allah dai Ya taimaki Raga da har ta gane gaskiya, da ita ma yanzu sai a hankali. Domin saurayin nata da ya zuga ta har ta yi wa Boda Taye (wato Giggs) rashin mutunci, yanzu ya koma yin muryar tallar fim ana ba shi N1,000. To, ka ga da ita ma yanzu ba a san me ta ke ciki ba. An dai ce in ka ga kare na sunsunar takalmi, dauka zai yi. Yanzu dai industiri ta zuba wa tsofaffin masoyan biyu na mujiya a ga ko daraktan zai kara fadawa ragar Zainab Raga.
Cewar wani furodusa: “A dai bi a hankali, Muhibbat na kallo daga restaurant din ta!”