KISHI, masu iya magana su ka ce, kumallon
mata. Duk da haka jarumtakar ’ya mace ita ce k'warewar ta wajen
iya sarrafa zuciyar ta a kan kishi, sau da yawa kishi kan sa mata
aikata katob'arar da za ta kai su ga aikin da-na-sani. To amma idan
aka yi dace mace ta iya daurewa ta sarrafa zuciyar ta, sai ka ga ta
kai ga samun nasara. Fim d'in ‘Yammaci’ na iya zama izna
ga mata masu zafin kishi a rayuwa.
Labarin ’yan mata biyu ne, k'awaye, wad'anda su ke da zafin
kishi, su ka kuma tsinci kan su cikin kogin son mutum d'aya.
Labarin ya fara ne salon da ba kasafai ake ganin finafinan Hausa
da irin shi ba. Fim d'in ya fara ne da wak'a (wadda Hassan da matar
sa Zuhra ke rerawa) Bayan wak'ar ne labarin ya fara, inda aka nuno
Ni’ima (Rukayya Umar) da Sa’adiyya (Rahma Ahmad) sun
dawo daga London, inda su ka je hutu tare da Alhaji (Aminu Hudu)
wanda kuma shi ne mahaifin Ni’ima, sannan kuma kawu ne ga
Sa’adiyya.
Sun shigo sun tarar da iyayen su mata, wato Hajara Usman (mahaifiyar
Ni’ima kuma matar Alhaji) da Jamila Haruna (mahaifiyar Sa'adiyya
kuma k'anwar Alhaji). Ni’ima ta nuna rashin jin dad'in ta
game da rashin samun damar halartar bikin babbar k'awar ta Zuhra
(Ummi Nuhu) da aka yi a Kano.
Bayan Ni'ima ta huta sai ta d'auki waya ta buga wa Zuhra ta yi
mata murna, har ta ce kada ta sake mijin ta ya kashe ta. Domin duk
ran da ya yi mata kishiya, to kamar ya kashe ta ne. Zuhra ta nuna
wannan maganar ta kishiya ai sai dai bayan ran ta.
Hassan (Sani Danja) shi ne angon Zuhra. Saboda irin son da Zuhra
ke yi masa, abin har ya wuce makad'i da rawa. Domin ko kyauta iyayen
ta su ka yi mata ba ta murna da ita, matuk'ar dai ba ta hannun mijin
ta ta biyo ba. Al’amarin kuwa ya na bak'anta wa mahaifiyar
ta rai.
Wata rana sakatariyar Hassan (Mansura Isah) ta saka masa wata wasik'a
ta soyayya a aljihun sa. Ganin wannan wasik'a da Zuhra ta yi ya
sa ta sha shinkafar b'era wai don ta mutu ta huta da zafin kishin
tunanin kishin da ta ke yi. Da k'yar aka samu likitoci su ka ceto
ran ta.
Hassan ya nemi sakatariyar tasa da ta rubuta wa Zuhura takarda
cewa wasa ta ke yi don ya samu ta hak'ura hankalin ta ya kwanta.
Da k'yar ta yarda ta rubuta. Ba a dad'e da yin haka ba Hassan ya
rasa aikin sa, rayuwa ta yi tsanani.
Rannan sai wani abokin sa (Ubale Wanke-wanke) ya ba shi shawarar
da ya tafi Legas wurin wani abokin su da ya yi kud'i. Haka kuwa
aka yi, cikin dare Hassan ya tsallake matar sa bayan ya rubuta mata
wasik'ar cewa shi ya tafi, amma ta jira shi ya tafi Legas, ya je
wajen abokin sa ne (Bashir K'aya).
A Legas, K'aya ya gabatar da shi ga ubangidan sa Alhaji (Aminu
Hudu). Aka ba shi aiki, ya murmure ya samu daula. A na cikin haka
ne Ni’ima ’yar Alhaji ta kamu da son Hassan.
Ala dole saboda gudun kada Alhaji ya k'wace dukiyar da ya samu,
Hassan ya yarda ya amshi goron soyayyar da Ni’ima (Ruk'ayya)
ta mik'o masa. Ya kuma yarda zai aure ta, amm duk a cikin rashin
sanin cewa k'awar matar shi ce da ya baro a Kano.
Al’amurran biki dai su ka kankama, an sa rana har an fara
raba katin gayyata, kwatsam sai Ni'ima ta ce za ta Kano. Hassan
ya nuna rashin amincewar sa, amma dole ta sa ya hak'ura.
Ni’ima ta isa Kano, ta je har gidan Zuhra ta kai mata katin
gayyata. Zuhura ta kama hanyar zuwa tashar mota sai aka yi mata
waya, ta na cikin amsa wayar sai fim d'in ya k'are.
Ko Zuhra na had'uwa da mijin nata a Legas? Me zai faru idan ta gano
cewa ashe mijin k'awar ta ne za ta aura?
SHARHI
Fim d'in ya yi kyau, sai dai ya na tattare da sark'ak'iya. Labarin
ya sami jigo mai k'arfi. Kazalika, jerin jaruman sun dace da rawar
da su ka taka. Tabbas a iya ba fim d'in tambarin “Da kyau.”
DARASI
Fim d'in ya na d'auke da darussa kamar haka:
Illar zafin kishi.
Illar rashin fad'in
gaskiya.
Illar abokan banza.
KURAKURAI
Duk yadda al’amari ya kai ga tsaruwa, ba za a rasa ’yan
kurakurai ba. Kurakuran da ke cikin ‘Yammaci’ sun had'a
da sautin hayaniyar mutane a lokacin d'aukar shirin. (Aminu Hudu)
ya d'an so ya wuce gona da iri, domin lokacin da aka kawo Hassan
wurin sa ba a nuna matsalar da ke damun sa ba sai kuma Alhaji ya
yi karaf ya kawo maslaha. Sannan ba a nuna dalilin da ya sa Hassan
ya k'i fad'in ya na da aure ba.
A saurari kashi na biyu
|