| Kamar yadda idan ajali ya zo ko babu ciwo
a mace, haka shi ma ajali na aure yake, wani lokacin ya kan faru ne
haka kawai ba tare da wasu ko wani dalili mai k'arfi ba. Wani lokacin
kuwa ya na faruwa ne saboda sakacin da mara lafiya ya ke yi wajen
k'in kula da bin shawarwarin da likita ya ba shi tun lokacin da aka
gano ya na da matsala, to shi ma haka ajalin zaman aure ya ke. Sau
tari ma’aurata na k'in bin shawarar da magabatan su su ke ba
su ne domin a samu zaman aure mai inganici.
Kamar yadda wani lokacin mara lafiya ya ke d'aukar lokaci ya na
jinya, wani lokacin ma har ya kai shi ga kwanciya a asibiti, daga
bisani kuma ya mace, haka shi ma zaman aure ya ke. Wani lokacin
da zarar an yi aure, to fa zama babu dad'i, yau ana gaban wannan
ana sasantawa gobe ana gaban wancan. Wani lokacin ma sai ta kai
ga mace ta yi yajin da za ta k'aurace wa gidan mijin nata, daga
bisani kuma auren ya mace.
Idan mu ka duba, za mu ga cewa zaman aure da mutuwar aure su na
kama da ajali na mutuwa a wani lokaci, amma kuma da akwai inda su
ke da bambanci, domin ita mutuwa ba ta da magani kwata-kwata, amma
ita mutuwar aure ta na da magani; idan har aka kiyaye wasu abubuwa
ana iya samun tsawon rayuwa ta aure, amma idan kuma aka yi masa
sakaci irin na mai fama da ciwon hawan jini ko ciwon siga ko kuma
sida, nan ta ke mutuwa ta na iya zuwa ta tauke shi.
Duk wani mai fama da ciwon siga, hawan jini ko sida ya na da wuya
ki ga cewa ya na wasa da duk wata shawara da likita zai ba shi domin
gudun kada mutuwa ta yi awon gaba da shi. Masu irin wannan ciwon
kullum su na cikin motsa jiki da kuma gudun cin duk wani abu da
likita ya hana su ci tare kuma da shan magani a daidai lokacin da
likita ya umurce su. Don haka su ke samun kuzari na tsawon lokaci
kafin mutuwa ta zo ta d'auke su.
Wannan duk shimfid'a ce ta yadda sakaci da kuma rashin bai wa ’ya’ya
mata mazajen da su ka dace da su da kuma lokacin da ya kamata mu
ba da su saboda yanayin zamani ya jawo karin k'ananan zawarawa da
auren su ya ke mutuwa a kowace rana ta Allah, kuma har yanzun nan
iyaye ba su fuskanci zurfin matsalar da irin wad'annan k'ananan
sauta-da-wawa su ke fuskanta ba da kuma bala’in da su ke k'ara
kawowa ga al’umma domin su kawo k'arshen wannan abin, don
haka kullum abin kamar k'aruwa ya ke yi.
A shekarun baya, idan har miji ya yi sakacin sakin matar sa mai
k'arancin shekaru, ko da laifin ta ko ba laifin ta, to tabbas sai
ya ga takaici, domin kafin ma ta gaba idda mazaje da dama su na
jiran ta. Don haka ne ma ake kiran duk wanda ya saki mace mai k'arancin
shekaru wawa, ita kuwa wacce aka sakar ake ce mata sauta-ga-wawa.
A wannan lokacin ya na da matuk'ar wahalar gaske ki ga mace ’yar
shekaru 16 zuwa 20 an sake ta, ko da kuwa mijin ta ya na fuskantar
matsalar zama da ita. Haka kuma idan har ma an saki mata masu irin
wannan shekaru, tabbas sai an samu cewa ta d'an jima a gidan miji
ba wai ta yi zama na d'an wasu watanni ne ko shekarun ba a gidan
mijin ba.
Irin wad'annan zawarawan a wancan lokacin ana samun su da kamun
kai, domin wata daga ranar da auren ta ya mutu har zuwa lokacin
yin wani auren nata ba za a gan ta a waje ko a titi ya na yawo unguwa
unguwa ba. Wannan ya sa har k'aramar bazawara, har ma da manyan
zawarawan wannan zamanin na da bayan an sake su har su yi wani aure
ba kowa ya sani ba. Sai dai kawai tsoffin mata da su ke unguwanni
ne su ke sani, su ma ganin su ne neman ma wasu mazan zawarawa ne.
Don haka duk gidan da aure ya mace a kunnen su, amma ba wai mace
idan auren ta ya mutu a gan ta a titi ta na tallar kan ta ba.
A yau, iyaye sun maida ’ya’yan su haja, duk wanda ya
zo ya taya. Idan yana tayawa da maik'o ko an gan shi da alamun mai
hannu da shuni ne a ba shi. A yau iyaye burin su shi ne su aurar
da ’yar su ga duk wanda ya nuna sha’awar sa ba tare
da binciken asalin sa da yanayin iya rik'e masu da kare mutuncin
’yar su ba. A yau iyaye sun k'yale ’ya’yan su
su na da k'arfi da ’yancin zab'ar wa kan su mazajen da za
su aura ba tare da ba su shawara ko cusa masu tarbiyyar ’ya’yan
su, su sukar masu dukkan ragamar rayuwar su ba.
A yau burin iyaye shi ne su dai su aurar da ’yar su ba tare
da ba ta tarbiyya ko ilimin addini da na zamani ba. A yau ya na
da matuk'ar wahalar gaske ki samu iyayen da za su aurar da ’yar
su su zaunar da ita su na mata hud'uba ak'alla na watanni uku kafin
zuwan aure domin su karantar da ita yadda rayuwar zaman aure ya
ke.
Wad'annan matsalolin da wasu da dama su ne zan kawo muku su idan
Allah Ya kai mu fitowa ta gaba domin ganin abin a zahiri yadda iyaye
su ke yin sakaci wajen aurar ta ’ya’yan su mata wanda
daga bisani kuma bayan namiji ya b'are ta, ya kwad'aita mata sanin
dad'in namiji, ya bambanta mata tsakanin ’ya mace da mace,
ya sauya mata fasali, ya kwantar mata da nonuwan da aka aurar masa
ita da su a tsaitsaye, daga bisani ya ingiza k'yeyar ta, wanda hakan
kuma ya sa idan ta dawo gida ta rik'a ganin da ita da uwar ta duk
d'aya su ke. Su kuma samari na unguwa da kuma alhazan banza su yi
yunk'urin maida ita filin sauke sha’awar su.
Sai dai kuma kafin wannan lokacin, ina son iyaye su yi karatun
ta-natsu musamman ga wad'anda ba su riga sun aurar da ’ya’yan
su domin ganin cewa masu neman ’ya’yan su da aure ba
wad'anda za su sako su ba ne bayan ’yan lokuta na zaman aure.
Su kuwa iyayen da aka riga aka sako nasu ’ya’ya, su
yi nazarin kuskuren da su ka yi domin kauce wa aukuwar hakan nan
gaba.
|