SHAFIN FARKO ...I.... GAME DA MU.....I....SHARHIN FIM.....I.....ADABI.....I.... WASIKU.....I... TUNTUBE MU

TABA KA LASHE
DAGA ZUCIYA
RAYUWAR IYALI
KWALLIYA DA GYARAN JIKI
GAJEREN KIRKIRARREN LABARI
 
A MUJALLAR & FIM TA WATAN GOBE
Me ya sa su MUTUWA DOLE suka kafa Kungiyar AHFIP?
'Karambanin' Farfesa Abdalla a Industiri! Ku biyo mu!>>

 
A FILM BY ABDALLA UBA ADAMU
DIRECTED BY
Bala Anas Babinlata
Visually Ethnographic Productions, 2009
Kano,
Northern Nigeria


YADDA AKA SO BUDE WA ’YAN FIM WUTA A JOS
AN ce tsautsayi in ya wuni ba ya kwana.
A ranar Asabar, 26 ga Yuni 2010, wasu ’yan fim su ka tsallake rijiya da baya a Jos, Jihar Filato.
Matsa nan don ci gaba.


RASHEEDA TA DEBO DA ZAFI A KATSINA
* An hana furodusoshi yin fim da ita, sannan darakta zai maka ta a kotu.
Matsa nan don ci gaba.

Zama Da Mata Sai Hakuri!



SAMARI ne biyu su na zaune a kofar gida su na hira, sai daya daga cikin su ya ce wa gudan, "Mata shegu ne!" Shi kuma dayan sai ya ce, "Ban da uwa ta." Ya fadi hakan ne a daidai lokacin da mahaifin sa ya fito daga cikin gida. Sai kuwa mahaifin nasa ya ce, "Ita ce ma babbar su!" Saboda a lokacin da ya fito daga gidan, matar sa ce ta gasa masa takaicin da ya ji tamkar ya bar garin.

Ga wadanda su ka karanci tarihin lokacin fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (S.A.W.) da sahabban sa game da yadda su ka yi rayuwa da iyalan su, mai karatu zai tabbatar da cewa sun yi matukar zaman hakuri da matan su. Shi kan sa Annabi da ya fi kowa a wannan duniya bai tsira ba daga hali da dabi'u irin na mata. Domin tarihi ya zo da yadda matan sa su ka yi ta yin abubuwa na takaici wanda sai da Allah (S.W.T.) Ya saukar da aya a kan su.

Ita mace, duk kudin ka, duk sarautar ka, duk ilimin ka da duk wani abu da ka ke takama da shi, ta na iya gwada maka cewa ba ka isa ba idan ta yi maka wani abu na takaici. Haka kuma mace duk karatun ta, duk mulkin ta, ko dukiyar ta da duk wata daukaka da Allah Ya yi mata, ta na nan dai a matsayin ta na mace. Domin akwai wasu halaye da dabi'un ta na asali da ba za ta taba iya kau da su ba. Shi ya sa a kullum mu ke sa-in-sa da kawaye na da su ke da tunanin cewa duk wani abu da namiji ya yi, mace ma za ta iya. Ni kuwa a kullum cewa na ke ba haka ba ne, domin halittar mace da ta namiji ma ba daya ba ce, balle kuma ta iya yin wani abu da ya fi dacewa da na maza.

Irin wadannan dabi'u da halin da mata ke da su ne, kuma wanda maza da damar gaske ba su sani ba ya sa ake ta yawan samun mace-macen aure da yanzu haka ya zama ruwan dare, musamman a nan arewacin Nijeriya. Da maza sun fahimci cewa mata fa a haka su ke, kuma haka Allah Ya yi su, domin hakan Ya ke son Ya gan su, don dacewa da hakan da su ka yi shi ya sa ma Ya ce wa maza su yi ta hakuri da mata, kuma Ya daukaka mazajen su a kan su, da ba za a samu mutuwar aure irin yadda ake samu yanzu ba.

Domin samari da dama su na dauka ne yadda su ke rayuwa ta samartaka cikin annashuwa da jin dadi, babu wani kalubale na zaman aure na yau da gobe, haka su ke zaton cewa za su zauna da matan su, wanda daga bisani idan aka yi auren kuma su ka ga wani dan canji ko kuma su ka wayi gari amarya ta gantsara masu wani takaici, sai ki ga sun kasa hakuri, wanda daga bisani aure ya ke mutuwa, mace ta zama karamar bazawara, ta na ta gararamba a gari.

Mace ce za ta bukaci wani abu daga wajen ka kai miji, amma ka na kawo mata ta na iya duba shi ta ce maka wanda ka saya ba mai kyau ba ne, ko kuma ta ce an buga maka a inda ka sayo, maimakon ta yi godiya. Mace ce za ta samu dan ta ta takura masa ya kara aure saboda wasu dalilai nata, amma da ita mijin ta zai yi mata kishiya saboda dalilin da ta ke bukatar dan ta ya kara aure, sai kuma ta tayar da jijiyar wuya. Haka kuma mace ce za ta shiga gaba wajen nemo wa wani aure idan zai kara, amma a duk lokacin da ta samu labarin cewa za a yi wa 'yar ta kishiya, daga wannan ranar da uwar amarya da duk wasu da su ka sa baki a wannan lamarin sun zama abokan gabar ta. Mace ce za ta iya tsayawa a aji ta karantar da Allah Ya ce Annabi ya ce, a bi aure a bi miji, amma da za ki ziyarce ta a gidan ta sai kin ga wasu abubuwa da ta ke yi, tamkar ba ita ba ce ta ke yin wa'azi ko karantawar a gaban jama'a ko dalibai.

Mace ta san da cewa Allah Ya hana wani abin da ta ke so saboda munin sa ko cutarwa da zai iya yi mata, amma muddin ran ta ya na kaunar wannan abin, sai ta aikata shi. Haka kuma duk kyan lamari, muddin ba ta da ra’ayin sa, wannan abin haramun ne a wajen ta. Dubi dai kishiya, babu mace Musulma da ba ta san cewa halas ba ne namiji ya kara aure idan ya cika sharuddan karawa, amma ba karamar mace mai imani ba ce za a yi mata kishiya kuma a same ta daidai ba. Haka kuma mata daidai ne za su tambayi fita kuma su je inda aka amince masu ba tare da sun kara da zuwa ko shiga makwafta ba, ba tare da la'akarin cewa ba su fa tambaya da nan din ba.

Babu shakka duk wani magidanci da ke zaune da matar sa ko matan sa, gaba dayan su su na hakuri da juna ne, amma shi maigida shi ya fi zaman hakuri, domin shi ne wanda nauyin gidan kacokam ya ke a hannun sa, don haka kuma ya na bukatar a yi masa ladabi daidai gwargwadon wanda mace za ta iya yi wa mijin ta. Haka kuma zai so idan ya nuna fushin sa na wani abu da aka yi masa mai radadi a ba shi hakuri, ko da kuwa shi ne ba shi da gaskiya. Da haka ne za a iya samun zaman aure mai inganci da kuma jin dadi.

Ya kamata mata su fahimci cewa babu wanda ya kamata ya yi shaidar halin su na kirki irin mazajen su. Domin ko iyayen mu ba za su iya fahimtar mu ba kamar mazan mu da mu ke zaune da su dare ba rana ba . Kuma mace ba za ta cika macen kirki abin alfahari ba sai idan mijin ta a duk lokacin da ya kalli fuskar ta zai ce mata: "Allah Ya yi albarka," kuma kullum tunanin sa shi ne yadda mutuwa za ta raba su.

Ya na da kyau maza su fahimci cewa idan har fiyayyen halitta zai yi hakuri da matan sa duk da irin abin da su ka yi masa na zamantakewar aure, ya na da kyau duk wani da namiji ya sanya a ran sa cewa aure fa ba ana nufin cewa gaba dayan sa nishadi ko annashuwa ba ne. Domin ta hanyar zaman aure Allah Ya na iya jarraba magidanta maza da mata ta hanyoyi da dama. Haka kuma wannan hakuri da kawaicin da Annabi (S.A.W.) da sahabban sa su ka yi na zama da matan su, ba ana nufin sun yi hakan ba ne domin kawai idan aka zo karanta tarihi a fade shi ba; Allah Ya nufe su da yin hakan ne domin mu ma na baya mu ga yadda wadanda su ka fi mu daraja da daukaka da duk wani abu na rayuwar duniya su ka zauna da matan su kuma su ka fuskanci matsaloli da su kuma su ka yi hakuri da su mu ma mu yi koyi da hakan.

Mafiya yawan samarin da su ke zuwa waje na don in ba su shawarwari game da aure, na fahimci cewa da daman su su na gina sha'awar auren nasu saboda soyayyar da su ke yi wa 'yanmatan su, ba wai su na sha'awar yin auren ba ne saboda sun shirya zaman auren. Don haka idan na tambaye su cewa, "Idan ka dawo gida ka samu matar ka ba ta yi maka abinci ba kuma ga komai na kayan abinci a gidan, kuma ka dawo da yunwa, ga kuma abokan ka ka shigo tare da su, yaya za ka yi?" kadan ne daga cikin su ke iya ba ni amsa mai gamsarwa. Kuma wannan matsalar kadan ce daga cikin matsaloli da hali da dabi'a irin na mace ya ke haifarwa.

Ya na da kyau maza su fahimci cewa akwai wasu halaye da dabi'u namu na mata wadanda ya na da wuya komai kudin namiji, komai zafin sa, komai sanyi da kuma sarautar sa da malantar sa ya hana mu aikata wanin abin. Don haka maza su bi shawara ko umurnin da Allah (S.W.A.) Ya ba su na zama da mu da hakuri, muddin ba a yi hakan ba a kullum magidanci ya na tare da takaici da kuma kuncin mata. Mu kuma mata ya kamata mu dubi Allah mu rika yin abin da ya kamata ga mazajen mu domin samun alherin da ke tattare da zamantakewar aure.

Sai dai ya na da kyau masu karatu, musamman maza, su fahimci cewa ba dukkan mata ne su ke da irin wadannan halayen da na ambata ba. Don haka kada wani ya ce, “Kun ji, ga shi matan da kan su su na fadin halin su marasa kyau, dukkan su haka su ke!” A’a, watakila kai mai karatu ba ka ma sani ba ko hali naka ne hakan.




Shafin Farko


An fara buga mujallar Fim (ISSN 1595-7780) a cikin Maris 1999. Ta na fitowa a kowane wata daga kamfanin INFORMART PUBLISHERS LTD., No. AK 6, Yoruba Road, Kaduna, Nijeriya. Ofishin mu a Kano: Ofishin mujallar Concern, 2nd Floor, Hadiza House, daura da Masallacin Umar Ibn Khattab, Zaria Road, Kano.
A aiko da dukkan wasiku ta adireshin mu na I-mel: mujallarfim@yahoo.com