| To
amma a shekarun nan da mu ke ciki, wani tsari ya
shigo cikin industiri na yin faifan wak'a da kowanne
mawak'in industiri ya kan yi domin masoya su san
shi, su san ashe shi ne ya yi wak'a kaza, har ma
ya samu mak'udan kud'i. Ta dalilin haka mawak'a
sun tashi daga sunan su na mutanen b'oye.
Mujallar Fim ta yi tattaki zuwa gidan su shahararriyar
zabiyar nan mai muryar azurfa, murya mai ratsa
zukatan masoya, mai tsima mutum, wato Maryam Saleh
Mohammed, wadda aka fi sani da Maryam Fantimoti.
“Akwatin Wak'a,” kamar yadda sarkin
barkwanci Ari Baba ya kira Maryam, a shirye ta
ke ta yi wak'a a kowane irin yanayi ko lokaci.
An ce ko barci ko gyangyad'i ka iske ta na yi,
kai ko a yanayin kuka ko dariya, tabbas in ka
ce ta rera maka wak'a, to za ta rera.
Mun tattauna da Fantimoti a gidan su da ke unguwar
Gyad'i-Gyad'i, kan titin Court Road da ke birnin
Kano, wato gidan iyayen ta, inda aka haife ta.
Ita Maryam ba ta zuwa ko'ina yawo; in ka gan ta
a waje, to an kira ta aiki ne ko kuma za ta zumunci,
amma ba za ka tarar da ita a situdiyo ba kamar
sauran mawak'a. Ga yadda hirar ta kasance.
Fim: Maryam Fantimoti, menene cikakken sunan
ki?
FANTIMOTI: Suna na Maryam Saleh Mohammed, wadda
aka fi sani da Fantimoti.
Shekarun ki na haihuwa nawa yanzu?
Ina da shekara 31 a duniya.
A ina aka haife ki?
An haife ni a nan inda ka ke hira da ni, gidan
mahaifi na, nan unguwar Court Road, Gyad'i-Gyad'i.
Iyayen ki ’yan asalin ina ne?
Mahaifi na kafin ya rasu d'an Kano ne, to daga
bisani Jigawa. Mahaifiya ta kuma ’yar asalin
Jihar Katsina ce, garin Funtuwa.
Ya batun karatun boko da na muhammadiyya?
Na’am, wannan tambayar ta yi kyau. Na yi
boko, iya firamare, sannan mahammadiyya har na
sauke K'ur’ani.
Me ya hana ki ci gaba da karatu daga firamare?
Dokar ’ya’yan gidan mu, ki na gama
firamare za a yi miki aure. An yi min aure a 1993,
Janairu, 1 ga watan.
A ina ne ki ka yi auren?
A nan Kano. Mijin da na aura d'an Warure ne, cikin
birnin Kano, amma mun zauna ne a unguwar Gwale.
Shekarun ku nawa tare da shi, kuma me ya faru
ku ka rabu, sannan ’ya’yan ku nawa
da shi in kun haihu tare?
Haba, sai ka ce wadda ta shiga siyasa? Ba zan
iya tuna ko shekarun mu nawa ba. Miji na ya rasu
ne, kuma mu na da ’ya’ya hud'u tare
da shi.
Kai, lallai ashe uwar ce ke ta sosai!
Da me ka ke tunani na?
’Ya’yan su na nan da rai?
Akwai Mohammed Auwal, Mohammed Jamilu, Hassana,
sai Hussaina - amma ita ta rasu. Su ne ma yanzu
ka gan su su na bi na kamar jela!
Ayya! Allah Ya jikan ta.
Amin summa amin.
Bayan mutuwar auren ki ba ki sake yin wani auren
ba?
Ah, na yi aure mana. Bayan miji na na farko ya
rasu, na auri wani d'an Hotoro. Shekarar mu uku
da shi mu ka rabu.
Shi ma mutuwar ya yi ko yaya?
Lokacin zama taren ne ya k'are.
Kun haihu da shi?
A’a.
To ya aka yi ki ka samu kan ki a harkar wakokin
industiri?
Na’am, wannnan tambayar taka ta yi min daidai.
Bayan miji na na farko ya rasu, sai na ji ya kamata
in d'an tab'a wata sana’a. To da yake da
ma tun ina Islamiyya na yi wak'ok'in yabon Manzon
Allah, wanda na kai wani matsayi da ba na tunani,
to mutuwar miji na sai na ji wak'ar fim d'in ‘Dawayya’
wacce Zuwaira ta rera, Ruk'ayya ta hau a fim d'in.
Wannan muryar ta ja hankali na, inda ni ma na
rera wak'a mai taken “Fantimoti”,
wak'a ta ta fim da na k'era ta farko kenan, na
kai wa Ali Nuhu, ya ji kuma ya yaba da murya ta,
ya ce ta yi. A lokacin kuma Rabi Mustapha ita
ce zabiyar mawak'a.
A wane fim aka sa wakar?
Ganin cewa na karb'u, sunan Fantimoti ya bi ni,
sai Ali Nuhu ya bar min wak'ar bai sa a fim ba.
Ka ji lokacin da na fara wak'a a industiri kenan.
Kin yi akalla wakoki nawa zuwa yanzu tun daga
lokacin da ki ka fara?
Zan iya cewa wak'ar siyasa, fim, bikin aure ko
na suna, yabon Manzon Allah, wak'ar nishad'i,
da sauran su, ak'alla zan iya k'iyastawa ina da
wak'ok'i dubu biyar.
Za ki iya lissafa mana wasu daga cikin su?
Ai ba sai na fad'a ba, wak'ar Fantimoti ba ta
b'uya; akwai irin su ita wak'ar “Fantimoti”,
“Mazaje” na marigayi Ahmed S. Nuhu,
‘Kusufi,’ ‘Uwargida,’
'Balagaggu,' ‘Zo Mu Zauna,’ ‘Maza
Jigida Mata Jigida,’ da kusan duk wasu wak'ok'in
maigida na sarkin mawak'a Yakubu Muhammad.
Me ya sa Yakubu ya zama ubangidan ki?
Ai dole a ce da mijin Iya baba, domin shi ne
ya fara rubuta min wak'a na rera a industiri;
wak'ar “Fantimoti” shi ne ya rubuta
min ita.
Duk a wakokin da ki ka yi a wane bangare ne ki
ka fi samun alheri?
Alhamdu lillahi, na gode wa Ubangiji, ai ni a
kowanne b'angare na samu alkhairi, kuma ina kan
samu har yanzu.
Kusan mawaka kowa ya na yin album na wakokin
sa. Me ya hana ki yi ke?
Ba komai. Amma ai yanzu na yi guda d'aya na yabon
Manzon Allah mai suna “Ceto”. D'aya
kuma wani furodusa ne a Minna ya ce min masoya
suna ta tambayar album d'i na, ya kamata ni ma
in yi, sai na shiga situdiyo na k'era wak'ok'i
goma sha biyu na ba shi na ce ya je ya d'au nauyin
fitar da shi. Sai ya ce, “Saboda me?”
Sai na ce masa ni ba ni da lokacin tsayawa in
fitar da wani album.
A ina za a fitar da album din?
Ni ban san wannan nan ba domin shi dai ya san
yadda zai tsara abin sa. Ni dai ba ni da lokaci.
Ana ta zuwa ana rijista da Hukumar Tace Finafinai
ta Jihar Kano. Ke kin je kin yi kuwa?
Ban je ba, kuma ban yi ba, domin ni dai ba kamfani
ne da ni ba, koyaushe ina gidan mu; in ka ga na
fita an bugo waya ne ana nema na sannan in fita.
Ai ba kamfani ba, wai a matsayin ki na mawakiya
tunda mawaka ma duk su na zuwa suna yi.
Ni ban sani ba, domin ban ga takarda a rubuce
ba, kuma ni komai nawa cikin tsari na ke yi. Kai,
ni tun da na ke jin mawak'a, na ke jin labarin
su, ban tab'a jin an ce Shata ko Garba Supa ko
D'ank'wairo ko Hassan Wayam da Barbani Choge sun
yi ko suna da rijista ba. Shi kenan kuma don mu
aka raina sai a ce sai mun yi wata rijista?
To ai can su watakila ba a Kano su ke ba, kuma
wannan dokar gwamnatin Kano ce, ke kuma ga ki
a Kano. Ba kya ganin ya kamata ki yi?
To sai dai ko don haka. Amma ni meye na zuwa
wani yin rijista - ni da zan yi aure?
Yaushe kuma, a ina, waye kuma mijin?
Kai dai akwai ka da shiga shirgin da ba naka
ba! Ina ruwan ka?
Ba kya so mu yi shirin zuwa bikin Fantimoti?
In lokacin ya zo za ku sani ai.
Ki na nufin ki ce duk abubuwan da hukumar su
Rabo ke yi ba ki da labari?
Ba sa gaba na, kuma ma ni ban san su ba; ina
dai jin wai wai.
Ki ce ba ki taba ganin Rabo ba ma?
A’a, na gan shi wurin k'addamar da wani
fim na Asibitin Malam Aminu Kano, ya je, har na
rera wa Rabo wak'a.
Meye burin Maryam Fantimoti a wannan harkar?
Alhamdu lillahi, burin Maryam ya cika, sai godiyar
Allah. Na samu d'aukaka da jama’a.
Menene kiran ki ko shawarar ki ga abokan sana’ar
ki maza da mata?
Babu abin da zan ce sai dai in ce masu Allah
ya kare mu a duk inda mu ke, mu so junan mu, mu
taimaki ’yan’uwan mu, mu cire k'yashi
da hassada.
Maryam Fantimoti, mun gode, sai Allah Ya kai
mu lokacin bikin ki.
Ni ma na gode, Maikatanga. |