SHAFIN FARKO ...I.... GAME DA MU.....I....SHARHIN FIM.....I.....ADABI.....I.... WASIKU.....I... TUNTUBE MU

TABA KA LASHE
DAGA ZUCIYA
RAYUWAR IYALI
KWALLIYA DA GYARAN JIKI
GAJEREN KIRKIRARREN LABARI
 
A MUJALLAR & FIM TA WATAN GOBE
Me ya sa su MUTUWA DOLE suka kafa Kungiyar AHFIP?
'Karambanin' Farfesa Abdalla a Industiri! Ku biyo mu!>>

 
A FILM BY ABDALLA UBA ADAMU
DIRECTED BY
Bala Anas Babinlata
Visually Ethnographic Productions, 2009
Kano,
Northern Nigeria


YADDA AKA SO BUDE WA ’YAN FIM WUTA A JOS
AN ce tsautsayi in ya wuni ba ya kwana.
A ranar Asabar, 26 ga Yuni 2010, wasu ’yan fim su ka tsallake rijiya da baya a Jos, Jihar Filato.
Matsa nan don ci gaba.


RASHEEDA TA DEBO DA ZAFI A KATSINA
* An hana furodusoshi yin fim da ita, sannan darakta zai maka ta a kotu.
Matsa nan don ci gaba.

RASHEEDA TA DEBO DA ZAFI A KATSINA


* An hana furodusoshi yin fim da ita, sannan darakta zai maka ta a kotu

Daga MOHAMMED ZAHARADDIN, a Katsina

DAUKAR shirin album din ‘Shaf-Shaf’ da fitaccen mawaki Sanusi Anu ya yi a Katsina kwanan baya, kai ka ce bikin auren wani gogarman dan fim ake yi. Haka dai furodusan ya tara gayyar ’yan wasa mata daga Kano don daukar shirin, aka yi kwana uku ana aikin, wanda darakta Aminu Mannir Keza Bokiti ya ba da umarni.

Kamar dai yadda a wani lokaci hayaniya da rikici kan faru a wajen daukar fim, haka ta faru a wajen daukar ‘Shaf-Shaf’. Hayaniya ce ta barke tsakanin Fauziyya Maikyau da jaruma Rasheeda Adam, har ta kai ga gorin mota, inda Rasheeda ta ce wa Maikyau: “Ai da ma ni na zo da ke a mota ta, saboda haka tun wuri ki nemi wanda zai maida ki Kano!”

Abin da ya faru kuwa shi ne, waka ce ake dauka, shi daraktan ya shirya cewa zai dauki kowa shi kadai. Saboda haka sai aka fara da Rashea. Ganin haka sai Fauziyya ta kasa hakuri ta ga ana daukar Rasheeda. Ga kuma wakar kowa so ya ke ya hau ta. Ta ce, “Wai darakta mutum daya kawai za a yi wakar da shi ne?” Fadin haka da ta yi ya bata wa Rasheeda rai. Sai kawai ta fara zage-zage. Inda ta ke shiga ba nan ta ke fita ba. Ta na cewa, “Ni fa yanzu na riga na daukaka, saboda haka ba shegiyar da za ta iya hana ni yin yadda na ke so!”

Ashe ita ma Fauziyyar ba kanwar lasa ba ce. Nan ta ke ta maida martani da zage-zage, da tona wa juna asiri. Irin dai maganganun da su ka rika yi wa juna ba kyau. A wannan dare dai aiki ya tsaya, domin kuwa Rasheeda duk ta birkita komai, karshe ma ta ki ci gaba da aikin, duk da yake an biya ta kudin aikin lakadan. Da kyar dai aka lallaba aka gama aikin.

Furodusan shirin, wato Rabi’u M. Yaro, ya bayyana yadda ya ji a kan abin da ya faru tsakanin jaruman biyu a lokeshin din sa. A hirar sa da wakilin mu, ya ce, “A matsayin Rasheeda na babbar ’yar wasa, bai kamata a ce irin haka na faruwa da ita ba. A ce duk lokacin da za a je aikin fim sai an samu matsala da ita?”

Me zai ce dangane da matakin da ’yan fim na Katsina su ka dauka a kan cewa ba za su kara kiran Rasheeda aiki ba? “Gaskiya ni na goyi bayan hakan. Dalili shi ne, duk mai son yi maka wasa da sana’a ya kamata tun wuri ka aje shi ko ma wanene. Gaskiya Rasheeda ta raina duk wani furodusa da ke Katsina, shi ya sa ta ke yin haka. Kuma saboda girman da ake ba ta ne. Don haka shawara ta a nan ita ce, ’yan fim din mu su kiyaye, saboda asara ba ta da dadi. Maganar nan da na ke maka ba mu gama aikin mu da ita ba ta kama hanya ta tafi. Ko da ta zo sai da ta ja mana rai, sannan ta matsa mu ka ida cika mata kudin ta sannan ta fara aikin”.

A WATA sabuwa kuma, wani fittacen darakta a garin Katsina ya maka Rasheeda Adamu Abdullahi a kotu, inda ya ce za ta zo ta amsa tambayoyi, sannan ta biya shi kudin da ya ba ta domin ta zo aikin shi amma ta ki zuwa, kuma ba ta maido masa kudin sa ba.

Mustapha B. Mohammed darakta ne da ya dade ya na harkar fim a Katsina. Shi ne darakatan finafinai irin su ‘Dufana’, ‘Tuntuben Harshe’ da kuma ‘Babban Zance’.

Daraktan ya shaida wa wakilin mu cewa, “Lallai Rasheeda za ta gurfana gaban kuliya a Katsina sakamakon rashin cika mana alkawari da ta yi... Abin ne ya zo da rainin hankili, shi ya sa za mu dauki mataki a kan ta. Sannan ina son wannan ya zama darasi ga duk wani dan fim da ya dauki sana’ar sa da muhimmanci”.

Shin daraktan ya nemi yin sulhu da ita kafin ya dauki matakin shari’a? Sai ya amsa da cewa, “Bari ka ji yadda abin ya faru. Na kira ta na gaya mata cewa ina da aiki da ita lokaci kaza. Ta amsa, ta kuma fada min ko nawa zan ba ta. Na dauki kudin ta duka na ba ta tun kafin lokacin ya yi. Sai da ranar ta zo, ga ’yan wasa kowa ya zo ita ba ta zo ba, sannan ba ta kira ni ta gaya min abin da ya hana ta zuwa ba har sai da na kira ta da kai na. Sai ta ke fada min cewa wai mahaifin ta ne ba shi da lafiya shi ya sa ba ta zo ba”.

Ko me ya hana su ba ta uzuri? “Kai, abin nata akwai rainin hankali! Lokacin da ta san na canza ta a aikin, kuma ta tabbatar na gama aikin, sai na kira ta inji inda aka kwana a kan maganar kudi na. Idan na kira sai ta ba kanwar ta a ce ba ta nan. Sai na samu wata waya da ba ta san layin ba na kira ta da shi, na ba wani ya yi magana da ita. Amma in ni na kira ta sai ta ba kanwar ta. Sannan kanwar ta din ta na cewa wai Rasheeda ta na Abuja. Sai ga shi da ’yan Katsina su ka je wata semina su ka hadu da ita a Kano. Kuma sun tabbatar min ba su ji wani ya yi mata jaje na marar lafiya ba. Wannan abin ya yi matukar bata min rai. Shi ya sa na kira lauya na, na shaida masa komai domin mu dauki mataki,” cewar daraktan.

Barista Aminu Kabir na Almakashi Chamber ya yi wa wakilin mu karin bayani kan wannan kara da za su shigar, inda ya ce, “Ba abin da zai hana mu shiga kotu da Rasheeda sai dai in ta kawo mana kudin mu. Domin ba wai kudin da mu ka ba ta ba za ta biya, a’a mu yanzu mu na kilemin ne. Saboda haka idan ta na da abin da ta ke takama da shi, to mu na jiran ta.”

Ko idan Rasheeda ta aiko da wadannan kudade ta banki kamar yadda aka tura mata kuma ta ba da hakuri za su hakura, kuma su ci gaba da harka da ita nan gaba?

Sai lauyan ya amsa da cewa, “To wannan yanzu ba zance ba ne da zan iya yanke hukunci, tunda mun rubuta takarda zuwa kotu kuma za a aika mata da sammace. Maganar kuma ci gaba da aiki da ita, wannan ya na wajen shi daraktan. Ni ba ni da ikon cewa komai a kan haka.”

Na goyi bayan kulle ’yan fim da Rabo ya yi, inji Rasheeda

* An dakatar da ita a Kaduna

KUNGIYAR masu shirya finafinai ta Jihar Kaduna ta dakatar da Rasheeda Adamu Adamu Abdullahi daga harkar fim har tsawon shekara daya saboda wasu kalamai da ta furta kan ’yan fim a wata hira da aka yi da ita a jaridar Sunday Trust. A hirar, wadda jaridar ta buga a ran Lahadi, 25 ga Yuli, 2010, fitacciyar jarumar kuma furodusa ta bayyana cewa ta na goyon bayan kulle ’yan fim a gidan wakafi da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta yi. Haka kuma ta ce duk dan fim din da ya yi kaura daga Kano zuwa wata jiha, to da ma can bare ne, ba dan Kano ba ne.

Idan kun tuna, daga 2007 zuwa yau hukumar a karkashin jagorancin Abubakar Rabo Abdulkareem ta gurfanar da ’yan fim da dama, manya da kanana, a kotu, inda daga can aka tura su gidan yari, yayin da wasu kuma aka yi masu babbar tara. Irin wadannan mutanen sun hada da Hamisu Lamido Iyan-Tama, Rabilu Musa Danlasan (Ibro), Adam A. Zango, Aminu Ala, da Aliyu A. Gora II.

Haka kuma dimbin 'yan fim, ciki har da ’yan asalin Jihar Kano, sun yi hijira daga Kano zuwa jihohi kamar Kaduna da Filato don tserewa daga musgunawa da kuma cin zarafin da ake yi masu.

A hirar da Sunday Trust ta yi da ita, Rasheeda ta kada baki ta ce: “Idan mutane sun kangare sun ki bin hukuma, shikenan sun amince da duk abin da zai biyo baya. Saboda haka a gani na duk wadannan da aka daure a gidan yari a dalilin kin bin umarnin hukumar, kawai abin da aka yi masu ya yi daidai. Yanzu a dube ni mana, me ya sa ni da wasu ’yan fim din da dama ba mu taba samun wata matsala da hukumar ba? Dalili shi ne mu mun zabi mu bi doka, sannan ni a nawa ganin a yanzu mun fi irin wadannan mutanen daraja a idon jama’a.”

A kan batun ’yan fim masu hijira kuma, Rasheeda ta yi nuni da cewa da ma can ’ya’yan baki ne su ka bar Kano su ka koma wasu jihohin. Ta ce: “Duk wadanda su ka bar jihar nan su ka koma wasu garuruwan wai da sunan samun inda ya fi dacewa su yi fim, da ma can baki ne, saboda haka kawai sun koma jihohin su ne inda za su iya yin abin da su ka ga dama. Mu da mu ke ’yan asalin Kano, mu na alfahari da hukumar tace finafinai kuma za mu ci gaba da bin doka da odar ta.

“Zan fada maki cewa yanzu hatta kayan aikin da mu ke yin fim da su sun inganta. Yanzu ba mu yin amfani da kyamarar wasan yara, kwalliyar mu da tufafin mu a fim da duk wasu abubuwa na yin fim sun inganta, ba domin komai ba sai don saboda sa hannun da hukumar tace fim din ta yi mana.”

’Yan fim da dama sun harzuka da wadannan kalamai. Su na ganin cewa Rasheeda ta watsa masu kasa a ido ne a daidai lokacin da su ke artabun yakin kwatar ’yancin su daga zaluncin da hukumar ta Rabo ta ke yi masu.

A ranar Talata, 27 ga Yuli, kungiya ta yi taron musamman a harabar kamfanin Crown Studio a Kaduna. A wurin, bayan an tattauna kan lamarin, sai aka yanke shawarar cewa an dakatar da Rasheeda daga harkar fim a duk fadin Jihar Kaduna har tsawon shekara daya. Wannan ya hada da hana ta fitowa a fim ko daukar fim ko yin gala ko kasuwancin fim a jihar.

An yi taron a karkashin jagorancin shugaban kungiyar, Yakubu Lere, sannan mahalarta taron sun hada da Ashiru Sani Bazanga, Ibrahim Sheme, Jamilu Dakandaka, Rabi'u Mohammed Rikadawa, Adam A. Zango, Abubakar Sani, Fatima Lamaj, Baban Chinedu, Jamilu Kochila, da sauran su da dama.






Shafin Farko


An fara buga mujallar Fim (ISSN 1595-7780) a cikin Maris 1999. Ta na fitowa a kowane wata daga kamfanin INFORMART PUBLISHERS LTD., No. AK 6, Yoruba Road, Kaduna, Nijeriya. Ofishin mu a Kano: Ofishin mujallar Concern, 2nd Floor, Hadiza House, daura da Masallacin Umar Ibn Khattab, Zaria Road, Kano.
A aiko da dukkan wasiku ta adireshin mu na I-mel: mujallarfim@yahoo.com