SHAFIN FARKO ...I.... GAME DA MU.....I....SHARHIN FIM.....I.....ADABI.....I.... WASIKU.....I... TUNTUBE MU

TABA KA LASHE
DAGA ZUCIYA
RAYUWAR IYALI
KWALLIYA DA GYARAN JIKI
GAJEREN KIRKIRARREN LABARI
 
A MUJALLAR & FIM TA WATAN GOBE
Me ya sa su MUTUWA DOLE suka kafa Kungiyar AHFIP?
'Karambanin' Farfesa Abdalla a Industiri! Ku biyo mu!>>

 
A FILM BY ABDALLA UBA ADAMU
DIRECTED BY
Bala Anas Babinlata
Visually Ethnographic Productions, 2009
Kano,
Northern Nigeria


YADDA AKA SO BUDE WA ’YAN FIM WUTA A JOS
AN ce tsautsayi in ya wuni ba ya kwana.
A ranar Asabar, 26 ga Yuni 2010, wasu ’yan fim su ka tsallake rijiya da baya a Jos, Jihar Filato.
Matsa nan don ci gaba.


RASHEEDA TA DEBO DA ZAFI A KATSINA
* An hana furodusoshi yin fim da ita, sannan darakta zai maka ta a kotu.
Matsa nan don ci gaba.

YADDA AKA SO BUDE WA ’YAN FIM WUTA A JOS


AN ce tsautsayi in ya wuni ba ya kwana. A ranar Asabar, 26 ga Yuni 2010, wasu ’yan fim su ka tsallake rijiya da baya a Jos, Jihar Filato. Kamar yadda aka sani, a duk inda aka ce ’yan fim su ka taru, masoyan su daga inda ba a tsammani su kan duraro domin kallon su. A wannan ranar an taru wajen daurin auren jarumi Sadiq Ahmed, wanda aka fi sani da Bala So,wanda aka yi a |ukur da ke Jihar Filato.

Kun san halin da garin ya ke ciki dai; kyas ake jira ka ga al’amurra sun yamutse. Ana cikin hada-hadar bikin, sai rigimar kudi ta hada wasu matasan ’yan fim sabon shiga, wadanda ko a industirin ma ba a san su sosai ba. Abu kamar wasa, rigimar ta girma har aka kai ga ba hamatta iska. Da ya ke garin cike ya ke da matakan tsaro, nan da nan kuwa wasu jami’an tsaro su ka dira. Da zuwan su, ba su ma san musabbabin rigimar ba, sai su ka ayyana cewa irin rikicin addini da aka saba yi ne a garin, wanda ya yi sanadiyyar salwantar dubban rayuka, ya ke neman tashi a wurin. Ai kuwa kan ka ce kwabo sai bindiga ta fara tashi. Nan fa taro ya fashe, kowa ya dafe keya cikin tsoron kada ya bakunci lahira. Wani matashin dan fim da ya halarci wurin cewa ya yi, “Ni wallahi dariya ma ta hana ni gudu. Yadda na ga su o’o duk girman su a industiri su na tsere da yaran su”.

Malam Aminu Hudu (Alma), shi ne tsohon shugaban kungiyar ’yan fim ta Jihar Filato, kuma sakataren kudi na kungiyar MOPPAN mai ci yanzu. Shi jami’an tsaro su ka kira a lokacin da al’amarin ya faru. A bayanin da ya yi wa wakilin mu kan ainihin yadda abin ya faru, da inda aka kwana, ya ce, “Wato ba wai an bude masu wuta a matsayin an harbi wani ko kuma an ci ma wani mutunci ba. ’Yar hatsaniya ce ta tashi a wurin daurin aure tsakanin yaran mu. To ganin wannan abin saboda yawan taron da ke wajen - saboda na dade a rayuwa ta ban ga daurin aure wanda ya samu jama’a irin wannan ba - saboda haka ganin irin wannan taro, a kokarin za a raba wannan fada na mutum biyu, sai ya zamanto jami’an tsaron da su ke wurin, da su ka ga cewa ba za su iya raba fadan ba, sai su ka yi harbi a sama. To ganin haka, bayan an watse kafin a dawo cikin garin Jos, sai hukumar tsaro ta SSS ta samu labari. Da ya ke da ma sun san cewa ni ne shugaban masu shirya fim na Jihar Filato, sai su ka kira ni a waya cewa an ji cewar ’yan fim ne su ke son su tayar da husuma. Sai na ce masu, ‘A’a, rigimar yara ce kawai. Amma saboda yawan jama’a, wajen a raba sai ake tsammanin wata hatsaniyar ce’.”

Daga baya dai jami’an tsaro sun gayyaci Alma da wadanda su ka yi rigimar zuwa ofishin su. Sai dai kuma an ci sa’a, domin tun kafin su isa har jami’an sun gano gaskiyar abin da ya faru. Don haka ko da su ka je, ba a bata lokaci ba aka sallame su.

’Yan fim da ke wurin a lokacin da wannan hayaniyar ta faru sun hada da Adam A. Zango, Ali Nuhu, Tanimu Akawu, Al-Amin Buhari, Zainab Indomi, da Fati Ladan.






Shafin Farko


An fara buga mujallar Fim (ISSN 1595-7780) a cikin Maris 1999. Ta na fitowa a kowane wata daga kamfanin INFORMART PUBLISHERS LTD., No. AK 6, Yoruba Road, Kaduna, Nijeriya. Ofishin mu a Kano: Ofishin mujallar Concern, 2nd Floor, Hadiza House, daura da Masallacin Umar Ibn Khattab, Zaria Road, Kano.
A aiko da dukkan wasiku ta adireshin mu na I-mel: mujallarfim@yahoo.com