SHAFIN FARKO ...I.... GAME DA MU.....I....SHARHIN FIM.....I.....ADABI.....I.... WASIKU.....I... TUNTUBE MU

TABA KA LASHE
DAGA ZUCIYA
RAYUWAR IYALI
KWALLIYA DA GYARAN JIKI
GAJEREN KIRKIRARREN LABARI
 
A MUJALLAR & FIM TA WATAN GOBE
Me ya sa su MUTUWA DOLE suka kafa Kungiyar AHFIP?
'Karambanin' Farfesa Abdalla a Industiri! Ku biyo mu!>>

 
A FILM BY ABDALLA UBA ADAMU
DIRECTED BY
Bala Anas Babinlata
Visually Ethnographic Productions, 2009
Kano,
Northern Nigeria


YADDA AKA SO BUDE WA ’YAN FIM WUTA A JOS
AN ce tsautsayi in ya wuni ba ya kwana.
A ranar Asabar, 26 ga Yuni 2010, wasu ’yan fim su ka tsallake rijiya da baya a Jos, Jihar Filato.
Matsa nan don ci gaba.


RASHEEDA TA DEBO DA ZAFI A KATSINA
* An hana furodusoshi yin fim da ita, sannan darakta zai maka ta a kotu.
Matsa nan don ci gaba.

JARUMAN AFRIKA: AN KARRAMA SU SANI DANJA A ABUJA


Fati, Ibro, Afakallah, Sani da Yakubu, kowanne da kambinsa na yabo

WATA kungiya mai zaman kan ta mai suna African Youth Society, wato Kungiyar Matasan Afrika, ta karrama wasu fitattun 'yan fim a Abuja, kamar yadda ta saba yi a duk shekara. Taron kaddamarwar, wanda aka gudanar a zauren taro na Hukumar Jami'o'i ta Kasa (National Universities Commission) a ranar Talata, 13 ga Yuli, 2010, ya samu halartar manyan baki daga ko'ina a cikin kasar nan. Kungiyar, wadda kudurin ta shi ne samar da nagartattun matasan da Afrika za ta yi alfahari da su wajen shugabanci, ta na da membobin da su ka fito daga kowace kasa a nahiyar.

Tun da farko a jawabin sa, babban sakataren kungiyar, Dakta Olusegun Sunday Adeleye, ya yi wa mahalarta taron jawabin maraba, inda ya dada jaddada manufofin kungiyar, kuma ya bayyana cewa kungiyar ta himmatu wajen ganin ta tallafa wa marasa galihu da marayu a cikin wannan al'umma. Ya kara da cewa kungiyar ta tsaya kyam wajen kwatar wa 'yan Afrika hakkokin su a ciki da wajen nahiyar.

Dangane da karramawar musamman da kungiyar ta yi wa 'yan fim din Hausa kuwa, shugaban ya ce masu shirin fim na Hausa sun kawo gagarumin ci-gaba a cikin al'ummar Hausawa, inda su ke amfani da basirar da Allah (SWT) Ya hore masu wajen ganin sun tallafa wa matasa wajen samun aikin dogaro da kai. Ya hore su da su ci gaba da wannan kyakkyawan taimako da su ke ba matasa.

'Yan fim da su ka karbi lambar yabon ta musamman su ne: Sani Musa Danja, Isma'il Na'Abba (Afakallah), Rabilu Musa Danlasan (Ibro), Yakubu Muhammad da kuma sabuwar jaruma Fati Ladan.

Da ya ke tofa albarkacin bakin sa jim kadan bayan karbar lambar yabon, Sani Danja, wanda shi ne shugaban kungiyar 'yan wasan fim ta Jihar Kano, ya bayyana farin ciki dangane da wannan karramawar da aka yi wa 'yan fim. Ya ce tabbas al'ummar kasar nan sun fara ganin hasken da masana'antar fim ke samarwa. Sannan ya hori 'yan'uwan sa a sana'ar da su hada kai wajen ganin an ciyar da kasar nan gaba.

Shi ma a nasa bangaren, Afakallah ya bayyana cewa ganin yadda finafinan Hausa ke tasiri a idon duniya a yau, ya na da kyau masu shirya fim su rika shirya finafinan da za su tafi da zamani da addini, gami da kyawawan al'adun kasar nan, musamman na Arewa. Dangane da yakar 'yan fim da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ke yi don ganin bayan harkar kuwa, Afakallah ya hori dukkan 'yan fim su kasance masu bin doka da oda. Ta nan ne, inji shi, za su cimma burin su. Ya kara da cewa duk wanda ke sana'a, to ya tsarkake zuciyar sa, kana kuma ya sanya Allah a gaba domin samun ingantaccen sakamako. Ibro kuwa ya yi matukar godiya ne ga kungiyar da ta karrama su. Ya kuma goyi bayan dukkan manufofin ta. Ya ce lokaci ya yi da ya kamata kowa ya natsu ya san halin da ya ke ciki, ya kuma yi aiki domin kawo ci-gaban al'umma.

Darakta Yakubu Muhammad ya nuna cewa kalamai sun yi karanci da zai nuna irin farin cikin sa game da irin wannan karramawar, musamman ma da yake a duk shekara sai kungiyar ta zabi fitattun al'ummar kasar nan da ma Afrika baki daya ta karrama su.

Fitaccen mawakin ya yi godiya kan yadda shugabannin kungiyar su ka sanya su cikin jerin wadanda su ka karrama. A karshe ya yi addu'ar Allah Ya zaunar da kasar nan lafiya, kuma ya shawarci 'yan fim da su fito kwan su da kwarkwatar su su mara wa wannan kungiyar baya.

Fati Ladan, wadda ita kadai ce mace a cikin 'yan fim da su ka samu lambar yabon, duk da cewa ta ratso garken fitattu ne, ta yi godiya ga Allah da Ya nuna mata ranar da aka ba ta wannan lambar yabon. Ta ce wannan ya nuna cewa lallai rabon kwado ba ya hawa sama. Amma a cewar ta, babu wanda ya yi zaton ta kai lokacin da za a karrama ta a idon duniya, domin ba ta dade da shiga harkar ba.

A karshe, ta yi addu'ar Allah Ya ciyar da masana'antar fim a nan Arewa gaba.

Cikin wadanda aka karrama bayan 'yan fim kuwa, har da ministan babban birnin tarayya, Sanata Bala Mohammed, da wasu manyan baki a ciki da wajen Nijeriya.






Shafin Farko


An fara buga mujallar Fim (ISSN 1595-7780) a cikin Maris 1999. Ta na fitowa a kowane wata daga kamfanin INFORMART PUBLISHERS LTD., No. AK 6, Yoruba Road, Kaduna, Nijeriya. Ofishin mu a Kano: Ofishin mujallar Concern, 2nd Floor, Hadiza House, daura da Masallacin Umar Ibn Khattab, Zaria Road, Kano.
A aiko da dukkan wasiku ta adireshin mu na I-mel: mujallarfim@yahoo.com