SHAFIN FARKO ...I.... GAME DA MU.....I....SHARHIN FIM.....I.....ADABI.....I.... WASIKU.....I... TUNTUBE MU

TABA KA LASHE
DAGA ZUCIYA
RAYUWAR IYALI
KWALLIYA DA GYARAN JIKI
GAJEREN KIRKIRARREN LABARI
 
A MUJALLAR & FIM TA WATAN GOBE
Me ya sa su MUTUWA DOLE suka kafa Kungiyar AHFIP?
'Karambanin' Farfesa Abdalla a Industiri! Ku biyo mu!>>

 
A FILM BY ABDALLA UBA ADAMU
DIRECTED BY
Bala Anas Babinlata
Visually Ethnographic Productions, 2009
Kano,
Northern Nigeria


YADDA AKA SO BUDE WA ’YAN FIM WUTA A JOS
AN ce tsautsayi in ya wuni ba ya kwana.
A ranar Asabar, 26 ga Yuni 2010, wasu ’yan fim su ka tsallake rijiya da baya a Jos, Jihar Filato.
Matsa nan don ci gaba.


RASHEEDA TA DEBO DA ZAFI A KATSINA
* An hana furodusoshi yin fim da ita, sannan darakta zai maka ta a kotu.
Matsa nan don ci gaba.

FIM DIN ‘BADALA’ YA TARA MALAMAN KANO


Shugaban Hukumar tace finafinai, Rabo

RIGIMAR da Abubakar Rabo ya ke yi da msu sana'ar finafinai ta fadada kwanan nan, inda har sai da wasu manyan malamai na Kano su ka zauna domin duba yiwuwar sasantawa tsakanin bangarorin biyu. Hakan ta faru ne a ranar Laraba, 21 ga Yuli, 2010. An yi taro na gaggawa ne a kan yadda za a warware wata babbar matsala da ke tsakanin shugaban na Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano da Alhaji Ado Abba mai kamfanin Arewa Fim Production, a game da fim din sa mai suna 'Badala'.

Taron wanda aka yi a dakin taro na Hukumar Shari'a ta Jihar Kano, wanda ke kan Titin Matan Fada, ya samu halartar dimbin masu ruwa da tsaki na kowanne bangare.

A jawabin sa na bude taron, shugaban Hukumar Zakka ta Jihar Kano, Farfesa Sani Zaharaddeen, ya ce, “Manufar wannan zama shi ne domin a samo hanyar da za a warware wata matsala da take tsakanin Malam Abubakar Rabo da kuma Alhaji Ado Abba, wanda shi Malam Rabo ya kawo mana cewa ga wata matsala da ta ke faruwa game da wani fim mai suna 'Badala', dan haka ya ke ganin a kawo shi ga Hukumar Shari'a a saka a gani don a ga me fim din ya kunsa, daga karshe a duba a ga ya dace da shari'a ko bai dace ba.”

Daga nan sai ya gabatar da Rabo domin ya fadi abin da ke cikin ran sa. A cikin jawabin nasa, Rabo ya ce, “Shi wannan fim da ake magana a kan sa, tun kafin zuwan mu an yi masa rijista. To, bayan zuwan mu sai shi wannan dan'uwa namu Ado Abba ya sake gabato da shi don a kara dubawa, kamar yadda ya ce, tunda an samu gyara. To, tun da farko da mu ka duba sai mu ka ga sunan fim din ma bai dace ba, wato 'Badala'. Sai mu ka ce ya mayar da shi 'Illar Badala', sannan mu ka ce ya koma ya cire wasu abubuwa da su ke ciki.

“To bayan ya kawo an sake dubawa sai mu ka ga cewar akwai dai matsalar, don haka mu ka tambayi masana a kan shari'a, su ka ce ko da an ba shi izini mu na da damar mu soke. Don haka mu ka ce mun soke izinin. To na dauka ya ji nasihar, sai kuma a 'yan kwanaki lauyan sa ya same mu da takarda. To wannan ya sa mu ka ga ya dace mu kawo maganar wannan gida”.

Ya kara da cewa, “Saboda irin abubuwan da fim din ya kunsa, shi kan sa daraktan fim din ya zo ya nemi afuwa a kan illar da ta ke ciki.”

Da Rabo ya gama, sai Kwamishina na Biyu a Hukumar Shari'a, Malam Umar Sani Fagge, ya mike ya yi bayani a kan yadda fim ya ke a Musulunci, inda daga karshe ya ce: “Finafinan da ake na Hausa sun saba wa addini da kuma al'adun mutanen Kano”.

Daga nan sai aka bai wa furodusan fim din dama don yin jawabi. Cikin jawabin nasa Alhaji Ado Abba ya ce shi a iya sanin sa ba haka su ka yi da Rabo ba. Ya ce abin da ya sani shi ne an gayyace shi a kan za a tattauna da malamai a game da wannan fim, “amma sai da mu ka zo sai mu ka ga cewa za a nuna fim ne. Kuma wannan ba abin mamaki ba ne, domin shi (Rabo) ya saba da irin wnanan abin”. Ya ci gaba da cewa, “Amma tunda abin ya kai ga haka, bisa wannan fuskoki da na gani na malamai na da iyaye na, na janye wannan abin. Saboda haka duk wani mataki da aka dauka a kan fim din, ni mai biyayya ne. Don haka ina ganin ba sai an kai ga nunawa ba”.

Daga karshe, ya yi kira ga Majalisar Malamai da ta rinka tsawatar wa Rabo kan abubuwan da ya ke yi, “domin mu 'yan Kano ne, kuma saboda mun ga yadda al'amura su ka lalace don haka mu ka shigo don mu ga yadda za a samu a gyara.”

Bayan ya gama jawabin ne sai aka ce za a nuna fim din. Amma an samu tsaiko saboda kan malamai ya rabu biyu, wasu su ka ce a nuna don a ga abin da ke ciki, wasu kuma su ka ce ai tunda shi mai fim ya ce ba sai an nuna ba duk abin da aka zartar ya amince, haka ya wadatar. A karshe dai masu ra'ayin sai an nuna su ka yi rinjaye, don haka aka kunna talabijin aka shiga kallo har tsawon awa guda, shugabannin Majalisar Malamai su na kallon fim din 'Badala'. Can da misalin karfe 1:00 aka gama kallo, kuma aka ba da dama mutane su yi bayani kan abin da su ka fahimta a fim din.

Mal. Umar Sani Fagge shi ne ya fara magana, inda ya ce, “Na ga fim din, sai dai ni a yadda na gani a kokarin yaki da badala, sai aka shigo da barna”. Ya kawo misali da cewar, “An yi rawa a wajen biki, kuma yin hakan zai sa yara su koya. Mace ta fito kan ta a bude, shi ma barna ne. An nuna wani Alhaji fasiki; shi ma ba daidai ba ne, don za a dauki manyan mutane fasikai. An koya harkar daudu a ciki”. Ya ci gaba da kawo sauran abubuwa, a karshe kuma ya nemi da a dakatar da fim din.

Daga nan sai Wazirin Kano, Malam Isa Waziri, ya yi dan takaitaccen jawabi, inda ya ce shi ya ga fim din, amma tunda jama'a su na da kokwanto a kan fim din, sai a koma ga hadisin Manzo (S.A.W.), wato ka bar abin da ka ke kokwanto ka koma ga wanda ba ka kokwanton sa. Don haka, a cewar sa, kawai a dakatar da wannan fim.

Shi kuma a tasa fahimta Dakta Bashir cewa ya yi: “A yadda na kalli fim din an yi kokarin niyya, amma hanyar da aka bi ita ta lalata lamarin. Don haka ba dakatar da fim za a yi ba, sai dai a san yadda za a yi hukuma ta ba da kudi a gyara fim din yadda zai yi daidai da shari'a.”

Shi kuma Babban Darakta na Hukumar Hisba, Malam Ibrahim Maibushira, ya ce dakatar da fim din shi ne mafi kyau, domin a cewar sa finafinan Hausa sun fi na Indiya illa ga al'ummar mu. Amma kuma Kwamishina na Daya a hukumar, Malam Yahaya Tanko, cewa ya yi, “Idan aka dakatar da wannan fim din, to akwai irin sa dubbai da su ke yaduwa a gidajen mu. Don haka a gyara wannan fim din don ya zama ma'auni ga masu yi a gaba”. Ya ce, “Na sha jin ana labarin yadda rayuwar 'yan daudu ta ke da kuma yadda ake bata yara a wajen talla, amma ban san yadda ake yi ba sai a yanzu”.

Kamar dain furodusan, shi ma daraktan fim din 'Badala,' Mohammed Garba Kabara, ya nuna cewa Rabo ya shara ta da ya ce wai ya je wajen sa ya nemi gafara kuma ya ce a dakatar da fim din. Ya ce ya kamata malamai su duba su ga yadda Rabo ya ke takura wa mutane wajen kamu da daurewa. “Wannan ya sa gaba daya harkar ta lalace, don haka mutane su ka bar gari su ka koma wani waje su na yi, kuma su na shigo da shi Kano, wanda a shekarun baya idan mutum ya yi fim a Ghana sai ya zo Kano zai yi masa rijista, saboda nan ne cibiyar kasuwar fim. Amma yanzu a Zaria za ka yi fim ka sake shi, kuma dole ya shigo Kano. Hakan ya sa kashi tara cikin goma na finafinan da ake sayarwa a Kano, shigo da su ake, ba su da rijista da Kano.”

Haka dai aka ci gaba da tattaunawa. A karshe, sai aka nemi Rabo da ya yi jawabin rufewa, amma sai shugaban Kwamitin Daraktoci na hukumar tace finafinai, Malam Rabi'u Inuwa Ibrahim, ya ce shi zai yi jawabi a madadin Rabo. A jawabin, ya ce, “Yanzu dai a wannan zama za mu iya cewa an yi sulhu kuma an fahimci juna. Amma maimakon a janye fim din, za a samar da kudi a yi gyara yadda fim din zai fita sosai ya zama fadakarwa ga al'ummar Musulmi… Nan gaba za mu samu lokaci mu zauna a samu maslaha da wadanda su ka tafi su ka bar gari don a samu a daidaita.”

Shi dai wannan yaro ya samu halartar manyan malamai da su ka hada da Sheik Isa Waziri (Wazirin Kano), Mal. Umar Sani Fagge, Mal. Yahaya Tanko. Mal. Ibrahim Maibushira, Farfesa Sani Zaharaddeen, da dai sauran manyan malamai.






Shafin Farko


An fara buga mujallar Fim (ISSN 1595-7780) a cikin Maris 1999. Ta na fitowa a kowane wata daga kamfanin INFORMART PUBLISHERS LTD., No. AK 6, Yoruba Road, Kaduna, Nijeriya. Ofishin mu a Kano: Ofishin mujallar Concern, 2nd Floor, Hadiza House, daura da Masallacin Umar Ibn Khattab, Zaria Road, Kano.
A aiko da dukkan wasiku ta adireshin mu na I-mel: mujallarfim@yahoo.com