TARON NEMAN MAFITA
A wani gagarumin yunkuri na samar da hadin kai tare da fidda jaki daga duma, ’yan kasuwar fim sun kafa sabuwar kungiya ta kasa baki daya, kuma sun fito da sababbin dokokin aiwatar da hadahadar finafinan Hausa.
Daga ALIYU A. GORA II, a Kaduna
LAHADI, 27 ga Yuni, 2010, rana ce mai cike da dimbin tarihi a fagen shirin fim na arewacin Nijeriya. Tun da aka kafa industiri, ba a taba samun lokacin da ’yan fim su ka taru wuri daya don neman mafita a kan wata matsala da ke addabar su, ko kuma sana’ar fim, domin duk wanda ya amsa sunan sa a hakar fim ya halarci wurin, kama daga ’yan kasuwa, furodusoshi, daraktoci, ’yan wasa, mawaka, editoci har zuwa makada. Akwai kuma Dakta Ahmed Sarari, wanda aka gayyata a matsayin wakilin Hukumar Tace Finafinai Ta Kasa, da sakataren babbar kun giyar ’yan fim, wato MOPPAN, na kasa Farfesa Umar Faruq Jibril, da wakilin Hukumar Kare Hakkin Mallaka ta Kasa, Mr. Bassey Ofem Usang.
An gudanar da taron ne a daya daga cikin dakunan taro na gidan Sardauna da ke Unguwar Sarkin Musulmi a Kaduna. An fara da misalin karfe 11:30 na rana. An kuma hada taron ne don tattaunawa kan matsalolin da ke addabar sana’ar finafinan Hausa, don neman mafita da samun yadda za a magance su. Wadanda su ka hada taron su ne ’yan kasuwar finafinan. Malam Rilwanu Yusuf (Smart) shi ne jagoran kiran taron. Daga cikin matsalolin da aka gabatar aka tattauna kan su a wajen taron akwai:
1. Yaki da masu satar fasaha
2. Tsayayyen farashin fim
3. Sakin finafinai a rana daya
4. Bukatuwar tsayyayen kwamiti na karbo basussuka da ’yan kungiya ke rike wa juna
5. Yiwuwar sanya finafinai a faifan DVD
6. Yadda za a fadada kasuwar finafinai
Furodusa, kuma shugaban kungiyar masu shirya fim na Jihar Kaduna, Alhaji Yakubu Lere, shi ne mai gabatarwa a taron. Bayan an bude taro da addu’a, kai-tsaye Lere ya fara gabatar da manyan baki, tare da umurtar su zuwa kan babban tebur. Manyan bakin sun hada da Dakta Ahmed Sarari, Farfesa Umar Faruq, Alhaji Aminu Hudu (Alma), Musa M. Jalingo, Alhaji Sani Mu’azu, Sukairaju Muhammad, Alhaji Musa Na Malam Kato, Alhaji Musa Na Saleh, Nasiru Salisu, Ashiru Sani Bazanga, Haj. A’isha Ahmed, da Mr. Bassey Ofem Usang.
Bayan sun zauna, sai mai gabatarwa ya mika lasifika ga daya daga cikin manyan ’yan kasuwar da su ka dauki nauyin taron, wato A. A. Rasheed, don ya gabatar da jawabin maraba. A. A. Rasheed ya nuna matukar jin dadin sa a kan yadda jama’a su ka amsa gayyatar da su ka yi masu. Ya ce hakan ya nuna jama’a a shirye su ke a hada kai don ceto harkar fim daga kuncin da ta shiga. A karshe, ya yi kira ga taro da a yi hakuri da juna, ta yadda za a samu kammala taron lafiya kowa ya koma gidan sa cike da farin ciki.
A nasa jawabin, babban bako mai jawabi, Dakta Ahmed Sarari, ya yi godiya ta musamman ga wadanda su ka dauki nauyin shirya taron. Ya kuma yi godiya a kan mutunta shi da aka yi na gayyatar sa a matsayin daya daga cikin manyan baki masu jawabi a taron. Ya kuma shawarci ’yan kasuwar da su ba hadin kai muhimmanci. A cewar sa, matsalolin da ke addabar kasuwar fim ba za a iya kau da su ba sai da cikakken hadin kai a tsakanin ’yan kasuwa. Da haka ya shawarci ’yan kasuwar da su kafa hadaddiyar kungiya ta kasa, ta yadda za su iya sani da kuma samun damar daukar matakin bai daya a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Farfesa Umar Faruq Jibril kuma, jawabin sa ya raja’a ne a kan sanin muhimmancin kasuwanci. Ya ce maganar satar fasaha da kusan za a ce ita ta tara jama’a a wurin, ba za a taba magance ta ba har sai furodusoshi da ’yan kasuwa sun san zurfin kasuwancin hajojin su. Ya ce idan aka yi la’akari da yawan jama’ar da ke bukatar kwafin finafinai su kalla, da wuya furodusa ya iya buga kasakasan da za su iya wadatar da bukatun masu kallo. Ya ce karancin yawan fim a kasuwa na ba da matukar gudunmuwa wajen ba barayin zaune damar satar fasaha, har su iya cin riba fiye da mai kaya. A karshe, ya shawarci furodusoshi da ’yan kasuwa da su rungumi zamani wajen sanya finafinan su a DVD, ko kuma a ci kasuwa a bar su da cizon yatsa.
Daga jawabin sa ne aka dakatar da taron na awa daya don a samu damar yin salla sannan a dawo a ci gaba. Bayan an dawo, sai gida ya yanke hukuncin ya kamata a kafa kungiyar ’yan kasuwa ta kasa baki daya kamar yadda Sarari ya ba da shawara tun farko. Ba tare da wata ja-in-ja ba, kowa ya amince. Nan take aka kafa babbar kungiyar ’yan kasuwar fim ta kasa, aka kuma zabi mutane bakwai a matsayin shugabannin ta na riko, wadanda za su tafiyar da kungiyar har na tsawon shekara daya sannan a yi zabe. An kuma ware ayyuka uku da ake so shugabannin su aiwatar a cikin shekara dayar. Ayyukan sun hada da samar wa kungiyar suna, da samar da kundin tsarin mulkin kungiyar, da kuma yi wa kungiyar rajista da gwamnati. Shugabannin rikon da aka zaba su ne:
1. Malam Rilwan Yusuf (Smart, Kaduna) - Shugaba
2. Muh’d Gali Na Malam Kato (Kano) - Mataimakin Shugaba
3. Aminu Hudu (Jos) - Sakatare
4. A’isha Mohammed (Maiduguri) Sakatariyar Kudi
5. Abdullahi Dan’asabe (Kaduna) - Sakataren Yada Labarai
6. Musa Jalingo (Kano) - Shugaban kwamitin yaki da satar fasaha
7. Sani Rainbow (Zamfara) - Ma’aji
Bayan an kammala gabatar da su, sai aka sake ba da damar kawo jawabai da ra’ayoyin jama’a. Faruku Nagudu, wanda daya ne daga cikin ’yan kwamitin sa kai na yaki da satar fasaha, shawara ya kawo cewa tunda yanzu al’amarin ya zama na kasa baki daya, ya kamata duk furodusan da zai fitar da fim din sa sai ya ba da kwafi 100 na fim din sa don samar wa kwamitin yaki da satar fasaha kudin gudanar da aikin su.
Rilwanu Yusuf (Smart) kuma kalubalantar Farukun ya yi da cewa maimakon furodusa ya ba da kwafi 100, ya kamata a yi koyi da takwarorin su na Kudu, wWato in furodusa zai fita da fim, zai biya N10,000.
Shi kuma jarumi Nura Hussain, shawara ya kawo cewa duk mutumin da ke cikin wannan sana’a, ya ba masu yaki da satar fasahar hadin kai. Ya ce amma ba dole, wanda ya ga ba zai iya ba ta rage ruwan sa, ba dai za a fasa saboda shi kadai ba. Isma’il Na’abba (Afakallahu) kuma cewa ya yi, “Duk wanda masu yaki da satar fasaha su ka kama da laifin satar fasahar wani furodusa, dan kasuwa ko mawaki, su daina cin shi tara. Kamata ya yi a gurfanar da shi a gaban kuliya, a yanke masa hukuncin zuwa gidan yari kawai. Wannan ya fi a rika karbar kudi. Domin in aka gane zancen kudi ne, wani ko nawa ake so zai biya, amma ba zai daina aikata laifin ba”.
Alhaji Musa Na Malam Kato kuma bayyana takaicin sa ya yi kan yadda masu yaki da satar fasahar ke gudanar da aikin su. Ya ce a duk lokacin da za su fita aiki sai sun nemi gudunmuwar kudi. Amma ya ce su kudin da su ke samowa kuma a ina su ke saka su? Ya ba da shawarar cewa tunda yanzu an yi tanadi na daukar nauyin su daga kungiya, to kamata ya yi a bude asusu a banki, duk lokacin da su ka fita aiki su ka samo kudi a zuba a ciki. Ya ce idan hakan ya dore, babu wanda za a rika tinkara da sunan ya ba da taimako nan gaba, tunda kungiya na da kudin ta a aje.
Bayan sauraren shawarwari da ra’ayoyin jama’a, sai aka bude gidauniyar neman taimako don tallafa wa wasu sassa na kungiyoyin fim da ke bukatar hakan. Kungiyoyin da za su ci gajiyar tallafin kuwa sun hada da Kwamitin Yaki Da Satar Fasaha, Kungiyar ’yan fim ta Kaduna a kan shari’ar membobin ta da Rabo, da sabuwar kungiyar ’yan kasuwa ta kasa da aka kafa. Nan take aka fara ba da gudunmmuwar kudade. Wadanda su ka ba da gudunmuwar su a wajen su ne:
1. Rilwan Yusuf (Smart) N100,000
2. Arra’us N80,000
3.Sani Rainbow N200,000
4: A. A. Rasheed Alkawari
5. Isiyaka Yellow N100,000
6. Musa Malam Kato N20,000
7. Murtala Madobi N50,000
8. Hamisu Arra’us N10,000
9. Abdulhadi N50,000
10. Chali N60,000
11. Ghali Na Malam Kato N20,000
12. Muhammad Nagari N100,000
13. A.S. Maikwai N20,000
14. Muhammad Sanusi N20,000
15. Shaba N50,000
16. Mamman Mutu-Ka-Raba N20,000
17. Babangida Jos N5,000
18. Aminu Mirror N5,000
19. MBJ N5,000
20. Nasiru Dararrafe N30,000
21.Jamilu Yellow N20,000
22. Danzaki N5,000
23. Fatima Lamaj Alkawari
24. Abubakar Abdullahi N20,000
25. Mai Jalingo N5,000
26. Achashe N20,000
27. Isiyaka Jalingo N10,000
28. Musa Jalingo N10,000
29. Aminu Hudu N200,000
Jimilla: N1,55,000
Bayan an rufe taron da addu’a da misalin karfe 5:36 na yamma, shugabannin rikon sun zauna. Su ka yanke shawarar kafa dokoki a kan kin bin dokar fitar da fim ba tare da ba da kwafi 100 na fim ba kamar yadda kowa ya amince tun farko don tallafa wa masu yaki da satar fasaha. Dokokin kuwa su ne:
1. Duk wanda zai fitar da fim sai ya fitar da kwafi 100 na fim din sa don tallafa wa masu yaki da satar fasaha.
2. Duk wanda ya ba da kwafi 100 za a ba shi rasidin shaidar ya bayar. Duk inda zai kai fim din kuma sai ya je da foto-kwafi na rasidin kafin ’yan kasuwa su karbi fim din.
3. Duk furodusan da ya saki fim ba tare da bin waccan doka ta sama ba, za a dakatar da fim din sa daga kasuwa.
4. Duk dan kasuwar da ya karbi fim din wanda bai cika ka’idar ware kwafi 100 ba, za a ci shi tarar N10,000.
5. Karya dokar da gangan sau daya tarar N10,000 ce. Karyawa sau biyu N20,000. Wanda ya karya sau uku kuma za a rufe shagon sa na sati daya da tarar N30,000.
Shugabannin sun zabi Umar na A.A. Rasheed a matsayin wanda zai karbi kwafi 100 a Kaduna ya ba da rasidi. A Kano kuma L. Isah ne na ofishin kungiyar ’yan kasuwa ta Kano zai karba ya ba da rasidi. Kafin su tashi taron da misalin karfe 9:00 na dare, ’yan kasuwar sun ajiye ranar Asabar, 3 ga Yuli, 2010, a matsayin ranar da za su zauna a Kano don ci gaba da tattaunawa a kan al’amurran sabuwar kungiyar.