FATIMA Sadisu KK jaruma ce da ake yayin ta a yanzu. To amma ba yanzu ta fara fim ba; ta samu ’yan shekaru ana bugawa da ita. Kuma ta sha wuya a industiri a wajen neman karbuwa ga furodusoshi da daraktoci. Idan kun tuna, tun a cikin 2007 mu ka ba ku tarihin ta, a wata guntuwar hira da mu ka yi da ita a matsayin ta na sabuwar ’yar wasa.
DAGA WANCAN LOKACI KUWA ZUWA YANZU, Fatima, wadda aka fi sani da Fati KK a fagen shirin fim, Allah Ya tarfa wa garin ta nono. Ta karbu ga masu abin, don haka ta fito a manyan finafinai da yawa. A yau da wuya a ce maka ga wani dan fim da bai san ta ba. Haka su ma masu kallo sun san ta, don kuwa ta na haskaka akwatunan talabijin din su.
Hasali ma dai ita ce ta ci gurbin Gwarzuwar Sabuwar Jaruma a bikin gasar finafinai ta SIM Awards da aka yi a Abuja a bana. Saboda haka ne mu ka sake waiwayar jarumar don jin dajin da ta ratso daga wancan lokacin zuwa yanzu, da yadda ta ke kallon kan ta a yanzu, da kuma burin ta a nan gaba kadan. ALIYU A. GORA II ne ya tattauna da ita a wurin daukar wani sabon fim na Ali Nuhu mai suna ‘Carjin Kwai’ a garin Kaduna kwanan nan, wanda ita Fati din ce jarumar shirin.
DUBA CIKAKKEN LABARI A MUJALLA.
Shafin Farko