SHAFIN FARKO ...I.... GAME DA MU.....I....SHARHIN FIM.....I.....ADABI.....I.... WASIKU.....I... TUNTUBE MU

TABA KA LASHE
DAGA ZUCIYA
RAYUWAR IYALI
KWALLIYA DA GYARAN JIKI
GAJEREN KIRKIRARREN LABARI
 
A MUJALLAR & FIM TA WATAN GOBE
Me ya sa su MUTUWA DOLE suka kafa Kungiyar AHFIP?
'Karambanin' Farfesa Abdalla a Industiri! Ku biyo mu!>>

 
A FILM BY ABDALLA UBA ADAMU
DIRECTED BY
Bala Anas Babinlata
Visually Ethnographic Productions, 2009
Kano,
Northern Nigeria


YADDA AKA SO BUDE WA ’YAN FIM WUTA A JOS
AN ce tsautsayi in ya wuni ba ya kwana.
A ranar Asabar, 26 ga Yuni 2010, wasu ’yan fim su ka tsallake rijiya da baya a Jos, Jihar Filato.
Matsa nan don ci gaba.


RASHEEDA TA DEBO DA ZAFI A KATSINA
* An hana furodusoshi yin fim da ita, sannan darakta zai maka ta a kotu.
Matsa nan don ci gaba.

Daga Ganin Kwakwaf...


DAGA FAUZIYYA D. SULAIMAN

MU na zaune a tsakar gida, kamar yanda mu ka saba kowace yamma in dai ba mu fita unguwa ba, ana ta hira da musu. Wata mata ta shigo gidan namu. Sai da ta iso tsakiyar gidan ta ce, “Gafaran ku dai masu gida, bako in babu sallama mugu ne!”

Gaba dayan mu mu ka kalle ta. ’Yar gajera ce, mai kiba, baka, fuskar ta da tsagu irin na bakin nan, ga wani a gefen fuskar ta hagu da dama, kan ta dauke da katon buhu. Ta na sanye da atamfa mai hoton igiya. Ta daure kan ta tamau da dankwali disko.

“Mu na ba da maganin ciwon kafa da na amosanin kashi da maganin hawan jini da na farin jini ko na sammu.” Ta na fari ta na waro idanuwa waje.

Daya daga cikin mu ta ce, “Allah Ya ba da sa’a...”

“A’a baiwar Allah! Ba na amsar kudi da yawa; sadakar ashirin kawai za ku ba da,” ta katse mai maganar.

“Laa! Ai kuwa Babata ta na ciwon kafa tun da dai na ji babu tsada,” Salame ta fada. Ba tare da jiin amsar mu ba, ta ce, “Mai magani kawo.” Ta kwance habar zaninta ta ciro aira ashirin.

Mai magani ta yi dariya, ta ce, “Bazamfara na ke, ba Mai Magani ba. Mu shiga daga daki na yi miki jawabi daki-daki.”

Babu musu, Salame ta shige dakin ta, Bazamfara na biye da ita.

Kafin su fito, Bintoto ma ta yanke shawarar karbar wa diyar ta na farin jini, don haka Bazamfara na fitowa ta ce, “Ni ma shigo ki ba ni na farin jini.” Su ka nufi dakin ta.

Ni kuwa na nufi Salame da gudu ina cewa, “Mu ga maganin, me ta ce miki ne?”

Ta ce, “A’a, ta ce kada a fada wa wani in dai ba haka ba maganin ba zai yi aiki ba.”

Na dage na dinga yi mata magiya har Tasalla da Indo na taya ni, amma sam ta ki fada mana. Ai kuwa ta na fitowa daga dakin Bintoto, Indo ma ta ce ita ma za a ba ta na sammu, don haka su ka shige dakin ta.

Na yi gurin Bintoto da gudu, ita ma ina tambayar ta abin da ya faru. Kememe ita ma ta ki gaya mini. Ina tsaye cike da jin haushin su, don yadda ka san ’yar jarida haka na ke da son ganin kwakwaf.

Sai na ji Tasalla ma ta kira ta dakin ta.

Na ce, “Au, haka ne abin!? Don dai naira ashirin wallahi zan ba da don na ji me ta ke ce muku.”

Ai kuwa ta na fitowa daga dakin Tasallah na ce, "Bazamfara shigo nan ni ma.”

Kowacce ta na tsaye a kofar dakin ta kamar an dasa su, sai zare idanuwa su ke yi. A gani na, haushi su ka ji da na kirawo ta, don ni ce mai karancin shekaru a cikin su; hasali ma amarya ce ni.

Mu na shiga ta bi dakin nawa da kallo, kana ta ce, "Hala ma amarya ce ke ko?”

Na ce mata, “E.”

“Kin yi bari kwanaki ko?”

Na ce mata, “E.”

Ta kuma cewa: “A dangin ki akwai Sani da Musa da Tabawa ko?”

Na kuma ce mata, “E.”

“Gidan ku ya na da kusurwa hudu, kuma ya na kallon gabas ko?”

Na kara amsa mata da “E.”

Sai ta fashe da dariya, ta ce, “Lallai yarinya Allah Ya so ki, don duk tarihin ki ya na tafin hannu na. Don haka idan ki ka yi wasa ba za ki haihu ba har abada don ki na da makiya; su ne su ka zubar miki da cikin nan, kuma sun sha alwashin ke da haihuwa har abada....”

Kai, zance dai ta dinga yi mini wanda har ba zan iya rikewa ba. Daga karshe ta ce, “Idan kin yi imani da Allah za ki mutu, to ki kawo wani abu zan taimaka miki.”

Na hadiyi wani yawu, don matar ta fara ba ni tsoro. Ganin na yi sototo da ni, alamar zan yi mata gardama, ya sanya ta dauko wani abu daga jakar ta ta busa a dakin. Sai na ji kamar an juya ni sama a kasa. Nan da nan na ce mata na yarda.

“To ki kawo wani abin da za a kai wa rauhanai su ji kamshin jikin ki gobe za a kawo miki kayan ki.”

Na yi narai-narai da ido.

Ta ce, “Kin ga, ke ba amarya ba ce? Ai ki na da kayan lefe. Bude sif din ki!”

Jiki na ya na kyarma na bude.

Ta yi wani murmushi, ta na kallon kayan. “Wanne ne ya fi tsada?”

Na nuna mata wani leshi da atamfa da joji.

Ta zaro su ta zuba cikin buhun nan, kana ta ce, “Saura gwal, ki ba ni shi ma kamshin jikin ki kawai za a ji.”

Na marairaice, na ce, “Allah, ba ni....”

“Karya ki ke yi! Idan na gan shi na dauko?”

Na ce mata, “E.”

Ai kuwa sai ta dauko kwanon Samira ta hudu a layi na uku ta bude, sai ga makullin adaka ta ta ciro. Ta je ta bude, ta daga murfin ta hau lalube. Jiki na ya dauki kyarma. Can sai ga dankunne na gwal da sarka a cikin akwatin sa.

Ta dube ni.

“Wannan mene ne? Na gaya miki mu na da rauhanai da ke gaya mana komai.”

Hawaye ya fara mini sintiri, don muddin ta dauki sarka da dankunnen nan na kade, domin dai na wata yaya ta ce na aro don jibi zan je suna dangin miji na.

“Malama, tunanin me ki ke yi? Ki kadaita Allah daya ki yi imani za ki mutu. Wallahi, billahillazi gobe za a dawo miki da kayan ki da rauhani ya ji kamshin jikin ki.” Ba ta jira jin abin da zan ce ba, ta kuma tura shi shi ma a jaka ta kulle buhun, ta dora a kan ta.

Na bi ta da sauri ido na ya na zubar da hawaye, na ce, “Ni dai da kin ba ni gwal din. Wallahi ba nawa ba ne!”

“Ke! Mu ba a kawo mana wargi. Idan na ba ki ma zan saka rauhanai su sace shi; gwara ma ki kyale a dawo miki da shi gobe. Ko na ba ki na turo su su sace din?" Da tsawa take maganar, don haka duk na tsure, na ce, “A’a, je ki kawai.”

Ina ji, ina kallo, ta fice daga dakin. Na bi ta zugwi-zugwi har ta fice daga gidan, ina kallon ta kamar yadda sauran ma ke tsaye sororo kamar an dasa su. Sai da ta yi kusan minti sha biyar da tafiya sannan na fasa kuka ina fadin, “Na shiga uku! Ta tafi da gwal din da na aro...”

“Ni ma ta amshi dubu goma na dashi,” inji Bintoto.

“Ni kuma rediyon maigida da sabuwar waya ta ta karba,” Indo ta ce.

“Ni kuma kudin sa da ya ke ba ni ajiya dubu shida ta karba,” inji Salame.

“Ni kuma ce mini ta yi matsiyaciya ce don haka kwanukan da aka kawo mini ajiya na samira ta dauka...”

Nan fa mu ka rude, kowa na kuka.

Shigowar mijin Indo ne ya sanya mu yin shiru. Ya hau tambayar mu, mu ka yi masa bayani. Ya yi salati, ya ce, “Lallai an damfare ku. Ai ’yar damfara ce. Ai haka su ke yi. Ku fito mu bi sawu.”

Nan fa mu ka bazama, kowa ya yi shiyyar sa. Ina tafe ina kuka, amma har Allah Ya gajiyar da mu ko mai kama da ita ba mu gani ba. Haka mu ka dawo gida, ina kuka ina fadin: “O ni! Daga ganin kwakwaf an sha da ni. Yanzu ya zan ce da mai gwal din nan?”

An karanta wannan labarin a Dandalin Hausa na Kungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA), Kano, a laburare na Murtala Muhammed, a Kano, a ran 2 ga Mayu, 2010.






Shafin Farko


An fara buga mujallar Fim (ISSN 1595-7780) a cikin Maris 1999. Ta na fitowa a kowane wata daga kamfanin INFORMART PUBLISHERS LTD., No. AK 6, Yoruba Road, Kaduna, Nijeriya. Ofishin mu a Kano: Ofishin mujallar Concern, 2nd Floor, Hadiza House, daura da Masallacin Umar Ibn Khattab, Zaria Road, Kano.
A aiko da dukkan wasiku ta adireshin mu na I-mel: mujallarfim@yahoo.com