SHAFIN FARKO ...I.... GAME DA MU.....I....SHARHIN FIM.....I.....ADABI.....I.... WASIKU.....I... TUNTUBE MU

TABA KA LASHE
DAGA ZUCIYA
RAYUWAR IYALI
KWALLIYA DA GYARAN JIKI
GAJEREN KIRKIRARREN LABARI
 
A MUJALLAR & FIM TA WATAN GOBE
Me ya sa su MUTUWA DOLE suka kafa Kungiyar AHFIP?
'Karambanin' Farfesa Abdalla a Industiri! Ku biyo mu!>>

 
A FILM BY ABDALLA UBA ADAMU
DIRECTED BY
Bala Anas Babinlata
Visually Ethnographic Productions, 2009
Kano,
Northern Nigeria


YADDA AKA SO BUDE WA ’YAN FIM WUTA A JOS
AN ce tsautsayi in ya wuni ba ya kwana.
A ranar Asabar, 26 ga Yuni 2010, wasu ’yan fim su ka tsallake rijiya da baya a Jos, Jihar Filato.
Matsa nan don ci gaba.


RASHEEDA TA DEBO DA ZAFI A KATSINA
* An hana furodusoshi yin fim da ita, sannan darakta zai maka ta a kotu.
Matsa nan don ci gaba.

Fati KK: Sa'a ta fi manyan kaya


BAYAN TA SHAFE
Bangon mujallar FIMSHEKARU A FAGEN SHIRIN FIM, FATI KK TA TAKI SA’A; YANZU ITA AKE YAYI.

SHIN MENENE ASALIN TA?

MENENE BURIN TA? SANNAN INA TA DOSA DAGA NAN?

FATIMA Sadisu KK jaruma ce da ake yayin ta a yanzu. To amma ba yanzu ta fara fim ba; ta samu ’yan shekaru ana bugawa da ita. Kuma ta sha wuya a industiri a wajen neman karbuwa ga furodusoshi da daraktoci. Idan kun tuna, tun a cikin 2007 mu ka ba ku tarihin ta, a wata guntuwar hira da mu ka yi da ita a matsayin ta na sabuwar ’yar wasa.

DAGA WANCAN LOKACI KUWA ZUWA YANZU,

Fatima, wadda aka fi sani da Fati KK a fagen shirin fim, Allah Ya tarfa wa garin ta nono. Ta karbu ga masu abin, don haka ta fito a manyan finafinai da yawa. A yau da wuya a ce maka ga wani dan fim da bai san ta ba. Haka su ma masu kallo sun san ta, don kuwa ta na haskaka akwatunan talabijin din su.
Matsa nan don ci gaba.


TARON NEMAN MAFITA


A wani gagarumin yunkuri na samar da hadin kai tare da fidda jaki daga duma, ’yan kasuwar fim sun kafa sabuwar kungiya ta kasa baki daya, kuma sun fito da sababbin dokokin aiwatar da hadahadar finafinan Hausa.

FIM DIN ‘BADALA’ YA TARA MALAMAN KANO


RIGIMAR da Abubakar Rabo ya ke yi da msu sana'ar finafinai ta fadada kwanan nan, inda har sai da wasu manyan malamai na Kano su ka zauna domin duba yiwuwar sasantawa tsakanin bangarorin biyu. Hakan ta faru ne a ranar Laraba, 21 ga Yuli, 2010. An yi taro na gaggawa ne a kan yadda za a warware wata babbar matsala da ke tsakanin shugaban na Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano da Alhaji Ado Abba mai kamfanin Arewa Fim Production, a game da fim din sa mai suna 'Badala'.

JARUMAN AFRIKA: AN KARRAMA SU SANI DANJA A ABUJA

WATA kungiya mai zaman kan ta mai suna African Youth Society, wato Kungiyar Matasan Afrika, ta karrama wasu fitattun 'yan fim a Abuja, kamar yadda ta saba yi a duk shekara. Taron kaddamarwar, wanda aka gudanar a zauren taro na Hukumar Jami'o'i ta Kasa (National Universities Commission) a ranar Talata, 13 ga Yuli, 2010, ya samu halartar manyan baki daga ko'ina a cikin kasar nan. Kungiyar, wadda kudurin ta shi ne samar da nagartattun matasan da Afrika za ta yi alfahari da su wajen shugabanci, ta na da membobin da su ka fito daga kowace kasa a nahiyar. Fati, Ibro, Afakallah, Sani da Yakubu, kowanne da kambinsa na yabo




An fara buga mujallar Fim (ISSN 1595-7780) a cikin Maris 1999. Ta na fitowa a kowane wata daga kamfanin INFORMART PUBLISHERS LTD., No. AK 6, Yoruba Road, Kaduna, Nijeriya. Ofishin mu a Kano: Ofishin mujallar Concern, 2nd Floor, Hadiza House, daura da Masallacin Umar Ibn Khattab, Zaria Road, Kano.
A aiko da dukkan wasiku ta adireshin mu na I-mel: mujallarfim@yahoo.com